Gida › Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce › Barci
Rayuwa da aiki
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da Barci
Ayoyin da masu karatu suka fi komawa gare su don wannan jigo (11), an ambace su gaba ɗaya daga Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa.
Zab 4:8
Zan kwanta in kuma yi barci lafiya, gama kai kaɗai, ya Ubangiji, kake sa mazaunina yă kasance lafiya lau.K Mag 3:24
sa’ad da ka kwanta, ba za ka ji tsoro ba; sa’ad da ka kwanta, barci zai yi maka daɗi.Zab 127:2
Banza ne ka farka da wuri ka koma da latti, kana fama don abincin da za ka ci, gama yakan ba da barci ga waɗanda yake ƙauna.Zab 91:5
Ba za ka ji tsoron razanar dare, ko kibiyoyi da suke firiya da rana ba,Mat 11:28
“Ku zo gare ni, dukanku da kuka gaji kuke kuma fama da kaya, zan kuwa ba ku hutu.K Mag 20:13
Kada ka so barci in ba haka ba za ka talauce; ka zauna a faɗake za ka kuwa kasance da sauran abinci.Zab 3:5
Na kwanta na yi barci; na kuma farka, gama Ubangiji yana kiyaye ni.Mat 8:24
Ba zato ba tsammani, sai wani babban hadari ya taso a tafkin, har raƙuman ruwan suka sha kan jirgin. Amma Yesu yana barci.Zab 121:3–4
Ba zai bari ƙafarka tă yi santsi ba, shi da yake tsaronka ba zai yi gyangyaɗi ba; tabbatacce, shi da yake tsaron Isra’ila ba ya gyangyaɗi ko barci.K Mag 19:23
Tsoron Ubangiji yakan kai ga rai. Sa’an nan mutum ya sami biyan bukata, ba abin da zai cuce shi.K Mag 6:22
Sa’ad da kake tafiya, za su bishe ka; sa’ad da kake barci, za su lura da kai; sa’ad da ka farka, za su yi maka magana.Waɗannan ayoyi ne da masu karatu suka fi komawa a wannan batu — ba koyarwa a kansa ba. Karanta kowanne a cikin surarsa.
Tushe
Ayoyin kowane jigo da tsarinsu: bayanan jigogi na OpenBible.info, bisa ƙuri’un masu karatu: OpenBible.info · CC BY 4.0
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.