Gida › Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce › Kuɗi
Rayuwa da aiki
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da Kuɗi
Ayoyin da masu karatu suka fi komawa gare su don wannan jigo (15), an ambace su gaba ɗaya daga Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa.
K Mag 22:7
Mawadaci yakan yi mulki a kan matalauci, mai cin bashi kuwa bawan mai ba da bashi ne.Ibr 13:5
Ku kiyaye kanku daga yawan son kuɗi, ku kuma gamsu da abin da kuke da shi, gama Allah ya ce, “Ba zan taɓa bar ka ba; ba zan taɓa yashe ka ba.”Luk 14:28
“In wani daga cikinku yana so ya gina gidan sama, ai, yakan fara zama ne, ya yi lissafin abin da ginin zai ci tukuna, don yă ga ko yana da isashen kuɗi da zai gama ginin.1Tim 6:10
Gama son kuɗi shi ne tushen kowane irin mugun abu. Waɗansu mutane, don tsananin son kuɗi, sun bauɗe daga bangaskiya suka kuma jawo wa kansu da baƙin ciki iri-iri.Mat 6:24
“Ba mai iya bauta wa iyayengiji biyu. Ko dai yă ƙi ɗaya, yă ƙaunaci ɗaya, ko kuwa yă yi aminci ga ɗaya, sa’an nan yă rena ɗayan. Ba dama ku bauta wa Allah, ku kuma bauta wa kuɗi gaba ɗaya.”K Mag 13:11
Kuɗin da aka same su a rashin gaskiya yakan ɓace da sauri, amma duk wanda ya tara kuɗi kaɗan-kaɗan za su yi ta ƙaruwa.K Mag 3:9–10
Ka girmama Ubangiji da dukan dukiyarka, ta wurin miƙa masa nunan fari na dukan amfanin gonarka; ta haka rumbunanka za su cika har su zuba, randunanka kuma su cika har baki da sabon ruwan inabi.M Had 5:10
Duk mai ƙaunar kuɗi ba ya samun isashe; duk ma ƙaunar dukiya ba ya ƙoshi da abin da yake samu. Wannan ma ba shi da amfani.K Mag 21:20
A gidan mai hikima akwai wuraren ajiya na abinci da mai masu kyau, amma wawa kan cinye duk abin da yake da shi.Luk 16:11
In fa ku ba amintattu ne cikin tafiyar da dukiya ta wannan duniya ba, wa zai amince muku da dukiya ta gaskiya?2Kor 9:6–7
Ku tuna fa, duk wanda ya yi shuki kaɗan zai girbe kaɗan, kuma duk wanda ya yi shuki da yawa, zai girbe a yalwace. Ya kamata kowa yă bayar bisa ga abin da ya yi shawara a zuciyarsa, ba tare da jin nauyi ko don dole ba, gama Allah yana son mai bayarwa da daɗin rai.Luk 12:15
Sai ya ce musu, “Ku lura fa! Ku tsare kanku daga dukan kowane irin kwaɗayi. Ran mutum ba ya danganta a kan yawan dukiyarsa ba.”K Mag 27:23–24
Ka tabbata ka san lafiyar garken tumakinka, ka mai da hankali ga garken shanunka; domin dukiya ba ta dawwama har abada, ba a kuma kasance da rawani daga tsara zuwa tsara.1Tim 6:17–19
Ka umarci waɗanda suke da arziki a wannan duniya kada su ɗaga kai ko su sa begensu a kan dukiyar da ba ta da tabbaci, sai dai su sa begensu ga Allah, wanda yake ba mu kome a yalwace don jin daɗinmu. Ka umarce su su yi nagarta, su wadatu cikin ayyuka nagari, su kuma zama masu bayarwa hannu sake da kuma masu niyyar yin taimako. Ta haka za su ajiye wa kansu dukiya a matsayin tushen mai ƙarfi don tsara mai zuwa, don su riƙi rai wanda yake na tabbatacce.1Tim 5:8
In wani bai kula da danginsa ba, musamman iyalinsa na kurkusa, ya mūsunta bangaskiya ke nan, ya kuma fi marar ba da gaskiya muni.Waɗannan ayoyi ne da masu karatu suka fi komawa a wannan batu — ba koyarwa a kansa ba. Karanta kowanne a cikin surarsa.
Tushe
Ayoyin kowane jigo da tsarinsu: bayanan jigogi na OpenBible.info, bisa ƙuri’un masu karatu: OpenBible.info · CC BY 4.0
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.