Bible Explorer

Gida › Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce › Shiri da makoma

Rayuwa da aiki

Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da Shiri da makoma

Ayoyin da masu karatu suka fi komawa gare su don wannan jigo (14), an ambace su gaba ɗaya daga Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa.

Irm 29:11Gama na san shirye-shiryen da na yi muku,” in ji Ubangiji, “shirye-shiryen cin gaba ba na cutarwa ba, shirye-shiryen ba ku sa zuciya da kuma na nan gaba.
K Mag 16:9’Yan Adam sukan yi shirye-shiryensu a zukatansu, amma Ubangiji ne yake da ikon cika matakansa.
K Mag 16:3Ka miƙa wa Ubangiji dukan abin da kake yi, shirye-shiryenka kuwa za su yi nasara.
K Mag 19:21Da yawa ne shirye-shiryen zuciyar mutum, amma manufar Ubangiji ce takan cika.
K Mag 21:5Shirye-shiryen mai aiki tuƙuru kan kai ga riba in kuwa ka cika gaggawa zai kai ga talauci.
Zab 37:5Ka sa kanka a hanyar Ubangiji; ka kuma dogara gare shi zai kuwa yi wannan.
K Mag 15:22Shirye-shirye sukan lalace saboda rashin neman shawara, amma tare da mashawarta masu yawa za su yi nasara.
K Mag 3:5–6Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka kada kuma ka dangana ga ganewarka; cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi, zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe.
Luk 14:28“In wani daga cikinku yana so ya gina gidan sama, ai, yakan fara zama ne, ya yi lissafin abin da ginin zai ci tukuna, don yă ga ko yana da isashen kuɗi da zai gama ginin.
Yaƙ 4:13–15Yanzu fa sai ku saurara, ku da kuke cewa, “Yau ko gobe za mu je wannan ko wancan birni, mu yi shekara a can, mu yi kasuwanci, mu ci riba.” Alhali kuwa ba ku ma san abin da zai faru gobe ba. Wane iri ne ranku? Ku kamar hazo ne da yake bayyana na ɗan lokaci sa’an nan yă ɓace. A maimakon haka, ya kamata ku ce, “In Ubangiji ya yarda, muna kuma a raye, za mu yi wannan ko wancan.”
K Mag 27:1Kada ka yi fariya a kan gobe gama ba san abin da ranar za tă kawo ba.
Ish 43:18–19“Ku manta da abubuwan da suka riga suka faru; kada ku yi tunanin abin da ya riga ya wuce. Duba, ina yi abu sabo! Yanzu yana faruwa; ba ku gan shi ba? Ina yin hanya a cikin hamada rafuffuka kuma a cikin ƙeƙasasshiyar ƙasa.
Zab 20:4Bari yă biya maka bukatan ranka yă kuma sa dukan shirye-shiryenka su yi nasara.
K Mag 6:6–8Ku tafi wurin kyashi, ku ragwaye; ku lura da hanyoyinsa ku zama masu hikima! Ba shi da jagora ba shugaba ko mai mulki, duk da haka yakan yi tanade-tanadensa da rani ya kuma tattara abincinsa a lokacin girbi.

Waɗannan ayoyi ne da masu karatu suka fi komawa a wannan batu — ba koyarwa a kansa ba. Karanta kowanne a cikin surarsa.

Tushe

Ayoyin kowane jigo da tsarinsu: bayanan jigogi na OpenBible.info, bisa ƙuri’un masu karatu: OpenBible.info · CC BY 4.0

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.