Bible Explorer

Gida › Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce › Girman kai

Rayuwa da aiki

Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da Girman kai

Ayoyin da masu karatu suka fi komawa gare su don wannan jigo (10), an ambace su gaba ɗaya daga Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa.

Fil 2:3Kada ku yi kome da sonkai ko girman kai, sai dai cikin tawali’u, ku ɗauki waɗansu sun fi ku.
K Mag 8:13Jin tsoron Ubangiji shi ne ƙin mugunta; ina ƙin girman kai da fariya, halin mugunta da kuma muguwar magana.
1Sam 2:3“Ka daina maganganu na girman kai ka kuma daina faɗin kalmomin ɗaga kai; gama Ubangiji Allah ne masani daga gare shi kuma ana auna ayyuka.
K Mag 16:18Girmankai yakan zo kafin hallaka, girman kai yakan zo kafin fāɗuwa.
Rom 12:3Gama ta wurin alherin nan da aka yi mini ne ina ce wa kowannenku. Kada yă ɗauki kansa fiye da yadda ya kamata, a maimakon haka bari yă auna kansa cikin natsuwa, gwargwadon baiwar bangaskiyar da Allah yi masa.
K Mag 16:5Ubangiji yana ƙyamar dukan zuciya mai girman kai. Ka tabbata da wannan. Ba za su kuɓuta daga hukunci ba.
Ish 13:11Zan hukunta duniya saboda muguntarta, mugaye saboda zunubansu. Zan kawo ƙarshe ga girman kan masu taƙama in kuma ƙasƙantar da ɗaga kan marasa tausayi.
K Mag 11:2Sa’ad da girman kai ya zo, sai shan kunya ta zo, amma hikima kan zo tare da ƙasƙantar da kai.
K Mag 29:23Fariyar mutum kan jawo masa ƙasƙanci amma mai sauƙinkai kan sami girmamawa.
K Mag 27:2Ka bar wani ya yabe ka, ba kai kanka ba; wani dabam, ba leɓunanka ba.

Waɗannan ayoyi ne da masu karatu suka fi komawa a wannan batu — ba koyarwa a kansa ba. Karanta kowanne a cikin surarsa.

Tushe

Ayoyin kowane jigo da tsarinsu: bayanan jigogi na OpenBible.info, bisa ƙuri’un masu karatu: OpenBible.info · CC BY 4.0

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.