Bible Explorer

Gida › Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce › Karimci

Rayuwa da aiki

Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da Karimci

Ayoyin da masu karatu suka fi komawa gare su don wannan jigo (11), an ambace su gaba ɗaya daga Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa.

Luk 6:38Ku bayar, ku ma sai a ba ku mudu a cike, a danƙare, har yă yi tozo, yana zuba, za a juye muku a hannun riga. Mudun da kuka auna da shi, da shi za a auna muku.”
Ayy M 20:35Cikin kowane abin da na yi, na nuna muku cewa da irin wannan aiki tuƙuru don mu taimaki marasa ƙarfi, muna tunawa da kalmomin da Ubangiji Yesu kansa ya ce, ‘Bayarwa ta fi karɓa albarka.’ ”
2Kor 9:7Ya kamata kowa yă bayar bisa ga abin da ya yi shawara a zuciyarsa, ba tare da jin nauyi ko don dole ba, gama Allah yana son mai bayarwa da daɗin rai.
K Mag 11:24–25Wani mutum kan bayar hannu sake, duk da haka yakan sami fiye; wani yakan riƙe abin da ba nasa ba, amma sai ya ƙarasa cikin talauci. Mutum mai kyauta zai azurta; shi da yakan taimake waɗansu, za a taimake shi.
K Mag 19:17Duk wanda yake kirki ga matalauta yana ba wa Ubangiji bashi ne, zai kuwa sami lada game da abin da ya yi.
2Kor 9:6Ku tuna fa, duk wanda ya yi shuki kaɗan zai girbe kaɗan, kuma duk wanda ya yi shuki da yawa, zai girbe a yalwace.
1Tim 6:17–19Ka umarci waɗanda suke da arziki a wannan duniya kada su ɗaga kai ko su sa begensu a kan dukiyar da ba ta da tabbaci, sai dai su sa begensu ga Allah, wanda yake ba mu kome a yalwace don jin daɗinmu. Ka umarce su su yi nagarta, su wadatu cikin ayyuka nagari, su kuma zama masu bayarwa hannu sake da kuma masu niyyar yin taimako. Ta haka za su ajiye wa kansu dukiya a matsayin tushen mai ƙarfi don tsara mai zuwa, don su riƙi rai wanda yake na tabbatacce.
Ibr 13:16Kada kuma ku manta yin aikin nagari da kuma taimakon waɗansu, gama da irin waɗannan hadayu ne Allah yake jin daɗi.
1Yoh 3:17In wani yana da arziki, ya kuma ga ɗan’uwansa cikin rashi, bai kuwa taimake shi ba, anya, ƙaunar Allah tana a cikinsa kuwa?
K Mag 22:9Mai bayarwa hannu sake shi kansa zai sami albarka, gama yakan raba abincinsa da matalauta.
K Mag 3:27Kada ka ƙi yin alheri ga duk wanda ya dace, sa’ad da kana iya yin haka.

Waɗannan ayoyi ne da masu karatu suka fi komawa a wannan batu — ba koyarwa a kansa ba. Karanta kowanne a cikin surarsa.

Tushe

Ayoyin kowane jigo da tsarinsu: bayanan jigogi na OpenBible.info, bisa ƙuri’un masu karatu: OpenBible.info · CC BY 4.0

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.