Bible Explorer

Gida › Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce › Amfani da lokaci da kyau

Rayuwa da aiki

Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da Amfani da lokaci da kyau

Ayoyin da masu karatu suka fi komawa gare su don wannan jigo (10), an ambace su gaba ɗaya daga Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa.

Afi 5:16Ku kuma yi matuƙar amfani da kowane zarafi, don kwanakin nan mugaye ne.
Zab 90:12Ka koya mana yawan kwanakinmu daidai, don mu sami zuciyar hikima.
Kol 4:5Ku zama masu hikima a yadda kuke ma’amala da waɗanda suke ba masu bi ba; ku kuma yi amfani da kowane zarafi.
Yaƙ 4:14Alhali kuwa ba ku ma san abin da zai faru gobe ba. Wane iri ne ranku? Ku kamar hazo ne da yake bayyana na ɗan lokaci sa’an nan yă ɓace.
M Had 3:1Akwai lokaci domin kowane abu, da kuma lokaci domin kowane aiki a duniya.
Zab 31:15Lokutana suna a hannuwanka; ka cece ni daga abokan gābana da kuma daga waɗanda suke fafara ta.
2Bit 3:8Amma kada ku manta da wannan abu guda ɗaya, abokaina ƙaunatattu. Ga Ubangiji kwana ɗaya kamar shekaru dubu ne, shekaru dubu kuma kamar kwana ɗaya ne.
Afi 5:15Sai ku yi hankali sosai da yadda kuke rayuwa, kada ku zama kamar marasa hikima, sai dai kamar masu hikima.
K Mag 6:6–8Ku tafi wurin kyashi, ku ragwaye; ku lura da hanyoyinsa ku zama masu hikima! Ba shi da jagora ba shugaba ko mai mulki, duk da haka yakan yi tanade-tanadensa da rani ya kuma tattara abincinsa a lokacin girbi.
Luk 14:28“In wani daga cikinku yana so ya gina gidan sama, ai, yakan fara zama ne, ya yi lissafin abin da ginin zai ci tukuna, don yă ga ko yana da isashen kuɗi da zai gama ginin.

Waɗannan ayoyi ne da masu karatu suka fi komawa a wannan batu — ba koyarwa a kansa ba. Karanta kowanne a cikin surarsa.

Tushe

Ayoyin kowane jigo da tsarinsu: bayanan jigogi na OpenBible.info, bisa ƙuri’un masu karatu: OpenBible.info · CC BY 4.0

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.