Gida › Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce › Ragwanci
Rayuwa da aiki
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da Ragwanci
Ayoyin da masu karatu suka fi komawa gare su don wannan jigo (15), an ambace su gaba ɗaya daga Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa.
K Mag 10:4
Ragwanci kan sa mutum yă zama matalauci, amma aiki tuƙuru kan ba da dukiya.2Tes 3:10
Ko ma a sa’ad da muke tare da ku, mun ba ku wannan umarni cewa, “In mutum ya ƙi yin aiki, kada a ba shi abinci.”K Mag 6:9
Har yaushe za ku kwanta a can, ku ragwaye? Yaushe za ku farka daga barcinku?K Mag 13:4
Rago ya ƙosa ya sami wani abu ainun amma ba ya samun kome, amma sha’awar mai aiki tuƙuru yakan ƙoshi sosai.Kol 3:23
Kome kuke yi, ku yi shi da dukan zuciyarku, sai ka ce ga Ubangiji kuke yi, ba ga mutum ba.K Mag 20:4
Rago ba ya noma a lokacin noma; saboda haka a lokacin girbi ba ya bukata samun kome.K Mag 6:6
Ku tafi wurin kyashi, ku ragwaye; ku lura da hanyoyinsa ku zama masu hikima!K Mag 21:25
Marmarin rago zai zama mutuwarsa, domin hannuwansa sun ƙi su yi aiki.K Mag 18:9
Wanda yake ragwanci a aikinsa ɗan’uwa ne ga wanda yakan lalatar da abubuwa.K Mag 20:13
Kada ka so barci in ba haka ba za ka talauce; ka zauna a faɗake za ka kuwa kasance da sauran abinci.K Mag 12:24
Hannuwan masu aiki tuƙuru za su yi mulki, amma ragwanci kan ƙarasa a aikin bauta.K Mag 14:23
Duk aiki tuƙuru yakan kawo riba, amma zama kana surutu kan kai ga talauci kawai.2Tes 3:11–12
Mun ji cewa waɗansunku suna zaman banza. Ba sa aikin kome; sai shisshigi kurum. Irin waɗannan mutane muna ba da umarni muna kuma gargaɗe su cikin Ubangiji Yesu Kiristi su natsu su kuma nemi abincin da suke ci.K Mag 22:13
Rago kan ce, “Akwai zaki a waje!” Ko kuma “Za a kashe ni a tituna!”K Mag 19:15
Ragwanci kan jawo zurfin barci, mutum mai sanyin jiki kuma yana tare da yunwa.Waɗannan ayoyi ne da masu karatu suka fi komawa a wannan batu — ba koyarwa a kansa ba. Karanta kowanne a cikin surarsa.
Tushe
Ayoyin kowane jigo da tsarinsu: bayanan jigogi na OpenBible.info, bisa ƙuri’un masu karatu: OpenBible.info · CC BY 4.0
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.