Gida › Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce › Aiki
Rayuwa da aiki
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da Aiki
Ayoyin da masu karatu suka fi komawa gare su don wannan jigo (13), an ambace su gaba ɗaya daga Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa.
Kol 3:23
Kome kuke yi, ku yi shi da dukan zuciyarku, sai ka ce ga Ubangiji kuke yi, ba ga mutum ba.K Mag 16:3
Ka miƙa wa Ubangiji dukan abin da kake yi, shirye-shiryenka kuwa za su yi nasara.K Mag 14:23
Duk aiki tuƙuru yakan kawo riba, amma zama kana surutu kan kai ga talauci kawai.K Mag 13:4
Rago ya ƙosa ya sami wani abu ainun amma ba ya samun kome, amma sha’awar mai aiki tuƙuru yakan ƙoshi sosai.K Mag 12:24
Hannuwan masu aiki tuƙuru za su yi mulki, amma ragwanci kan ƙarasa a aikin bauta.2Tes 3:10–12
Ko ma a sa’ad da muke tare da ku, mun ba ku wannan umarni cewa, “In mutum ya ƙi yin aiki, kada a ba shi abinci.” Mun ji cewa waɗansunku suna zaman banza. Ba sa aikin kome; sai shisshigi kurum. Irin waɗannan mutane muna ba da umarni muna kuma gargaɗe su cikin Ubangiji Yesu Kiristi su natsu su kuma nemi abincin da suke ci.Far 2:15
Ubangiji Allah ya ɗauko mutumin ya sa shi cikin Lambun Eden domin yă nome shi, yă kuma lura da shi.Zab 90:17
Bari alherin shugabanmu Allah yă kasance a kanmu; ka albarkaci mana aikin hannuwanmu, I, ka albarkaci aikin hannuwanmu.M Had 9:10
Duk abin da hannunka yake yi, ka yi shi da dukan ƙarfinka, gama a cikin kabari in da za ka, babu aiki ko shirye-shirye, ko sani, ko hikima.1Tim 5:8
In wani bai kula da danginsa ba, musamman iyalinsa na kurkusa, ya mūsunta bangaskiya ke nan, ya kuma fi marar ba da gaskiya muni.2Tim 2:6
Manomi mai aiki sosai ya kamata yă zama na fari wajen samun rabon amfanin gona.K Mag 12:11
Duk wanda ya nome gonarsa zai sami abinci a yalwace, amma shi da yake naushin iska marar azanci ne.M Had 3:12–13
Na san ba abin da ya fi wa mutane kyau fiye da su ji daɗi su kuma yi alheri yayinda suke da rai. Cewa kowa yă ci, yă sha, yă kuma ji daɗi cikin dukan aikinsa, wannan kyautar Allah ce.Waɗannan ayoyi ne da masu karatu suka fi komawa a wannan batu — ba koyarwa a kansa ba. Karanta kowanne a cikin surarsa.
Tushe
Ayoyin kowane jigo da tsarinsu: bayanan jigogi na OpenBible.info, bisa ƙuri’un masu karatu: OpenBible.info · CC BY 4.0
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.