Gida › Shahararrun ayoyin Littafi Mai Tsarki › Karin Magana 3:5–6
Ayar Littafi Mai Tsarki · SRK
Karin Magana 3:5–6
5Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka kada kuma ka dangana ga ganewarka;
6cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi, zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe.
Karanta dukan babin: Karin Magana 3
A cikin mahallinsa
2gama za su ƙara maka tsawon rai da shekaru masu yawa su kuma kawo maka wadata.
3Kada ka bar ƙauna da aminci su rabu da kai; ka ɗaura su kewaye da wuyanka, ka rubuta su a allon zuciyarka.
4Sa’an nan za ka sami tagomashi da kuma suna mai kyau a gaban Allah da kuma a gaban mutane.
5Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka kada kuma ka dangana ga ganewarka;
6cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi, zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe.
7Kada ka zama mai hikima a ganinka; ka ji tsoron Ubangiji ka kuma guji mugunta.
8Wannan zai ba wa jikinka lafiya yă kuma adana ƙasusuwanka.
9Ka girmama Ubangiji da dukan dukiyarka, ta wurin miƙa masa nunan fari na dukan amfanin gonarka;
Da Turanci
Trust in the LORD with all your heart, and lean not on your own understanding; in all your ways acknowledge Him, and He will make your paths straight.Nassoshi masu alaƙa
Sassan da masu karatu suka fi danganta wa da wannan.
Ka sa kanka a hanyar Ubangiji; ka kuma dogara gare shi zai kuwa yi wannan.“Amma mai albarka ne mutumin da yake dogara ga Ubangiji, wanda ƙarfin halinsa yana daga Ubangiji. Za su zama kamar itacen da aka dasa kusa da ruwa wanda ya miƙa saiwoyinsa zuwa cikin rafi. Ba ya jin tsoro sa’ad da zafi ya zo; ganyayensa kullum kore suke. Ba shi da damuwa a shekarar fări ba ya taɓa fasa ba da ’ya’ya.”Duk mai dogara ga kansa wawa ne, amma duk wanda yake tafiya da hikima zai zauna lafiya.Ka dogara ga Ubangiji ka kuma aikata alheri; yi zama cikin ƙasar ka kuma more makiyaya mai lafiya.Ku dogara a gare shi a duk lokuta, ya mutane; ku faɗi albarkaci bakin zukatanku a gare shi, gama Allah ne mafakarmu. SelaZa ka kiyaye shi da cikakken salama shi wanda ya kafa zuciyarsa gare ka, domin ya dogara a gare ka. Ku dogara ga Ubangiji, gama shi Ubangiji, ne madawwamin Dutse.Tabbatacce Allah shi ne mai cetona; zan dogara gare shi ba kuwa zan ji tsoro ba. Ubangiji, Ubangiji, ne ƙarfina da waƙata; ya zama mai cetona.”Ka natsu a gaban Ubangiji ka kuma jira da haƙuri gare shi; kada ka tsorata sa’ad da mutane ke nasara a hanyoyinsu, sa’ad da suke aikata mugayen shirye-shiryensu.Tushe: OpenBible.info, CC BY 4.0 · Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi