Gida › Shahararrun ayoyin Littafi Mai Tsarki › Karin Magana 18:22
Ayar Littafi Mai Tsarki · SRK
Karin Magana 18:22
Duk wanda ya sami mace ya sami abu mai kyau ya kuma sami tagomashi daga Ubangiji.
Karanta dukan babin: Karin Magana 18
A cikin mahallinsa
19Ɗan’uwan da aka yi wa laifi ya fi birni mai katanga wuyan shiryawa, kuma faɗace-faɗace suna kama da ƙofofin ƙarfe na fada.
20Daga abin da baki ya furta ne cikin mutum kan cika; girbi daga leɓunansa kuma yakan ƙoshi.
21Harshe yana da ikon rai da mutuwa, kuma waɗanda suke ƙaunarsa za su ci amfaninsa.
22Duk wanda ya sami mace ya sami abu mai kyau ya kuma sami tagomashi daga Ubangiji.
23Matalauci kan yi roƙo da taushi, amma mawadaci kan amsa da kakkausar murya.
24Mutum mai abokai masu yawa kan lalace, amma akwai abokin da yakan manne kurkusa fiye da ɗan’uwa.
Da Turanci
He who finds a wife finds a good thing and obtains favor from the LORD.Nassoshi masu alaƙa
Sassan da masu karatu suka fi danganta wa da wannan.
Ana gādon dawakai da wadata daga iyaye ne, amma mace mai basira daga Ubangiji ne.Mace mai halin kirki rawanin mijinta ne, amma mace marar kunya tana kama da ciwo a ƙasusuwansa.Ka more rayuwa da matarka, wadda kake ƙauna, dukan kwanakin nan marasa amfani da Allah ya ba ka a duniya. Gama wannan ne rabonka a rayuwa da kuma na faman aikinka a duniya.Amma da yake fasikanci ya yi yawa, ya kamata kowane mutum yă kasance da matarsa, kowace mace kuma da mijinta.Ubangiji Allah ya ce, “Bai yi kyau mutumin yă kasance shi kaɗai ba. Zan yi masa mataimakin da ya dace da shi.”Yaƙub ya gudu zuwa ƙasar Aram; Isra’ila ya yi bauta don yă sami mata, domin kuma yă biya, sai da ya yi kiwon tumaki.Gama duk wanda ya same ni ya sami rai zai kuma sami tagomashi daga Ubangiji.Saboda haka Yaƙub ya yi bauta shekaru bakwai domin a ba shi Rahila, amma shekarun suka zama kamar ’yan kwanaki ne kawai gare shi saboda ƙaunar da yake mata. Sa’an nan Yaƙub ya ce wa Laban, “Ba ni matata. Lokacina ya cika, ina kuma so in kwana da ita.”Tushe: OpenBible.info, CC BY 4.0 · Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi