Gida › Shahararrun ayoyin Littafi Mai Tsarki › Karin Magana 13:11
Ayar Littafi Mai Tsarki · SRK
Karin Magana 13:11
Kuɗin da aka same su a rashin gaskiya yakan ɓace da sauri, amma duk wanda ya tara kuɗi kaɗan-kaɗan za su yi ta ƙaruwa.
Karanta dukan babin: Karin Magana 13
A cikin mahallinsa
8Arzikin mutum zai iya kuɓutar da ransa, amma matalauci ba ya jin barazana.
9Hasken masu adalci kan haskaka ƙwarai, amma fitilar mugaye mutuwa take.
10Girmankai kan jawo faɗa ne kawai, amma hikima tana samuwa a waɗanda suke jin shawara.
11Kuɗin da aka same su a rashin gaskiya yakan ɓace da sauri, amma duk wanda ya tara kuɗi kaɗan-kaɗan za su yi ta ƙaruwa.
12Sa zuciyar da aka ɗaga zuwa gaba kan sa zuciya tă yi ciwo, amma marmarin da aka ƙosar yana kamar itacen rai.
13Duk wanda ya rena umarni zai ɗanɗana ƙodarsa, amma duk wanda ya yi biyayya da umarni zai sami lada.
14Koyarwar mai hikima maɓulɓulan rai ne, mai juyar da mutum daga tarkon mutuwa.
Da Turanci
Dishonest wealth will dwindle, but what is earned through hard work will be multiplied.Nassoshi masu alaƙa
Sassan da masu karatu suka fi danganta wa da wannan.
Gādon da aka samu da sauri a farkon farawa ba zai zama mai albarka a ƙarshe ba.Dukiyar da aka samu a hanyar da ba tă dace ba, ba ta da albarka, amma adalci kan ceci mutum daga mutuwa.Tushe: OpenBible.info, CC BY 4.0 · Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi