Gida › Shahararrun ayoyin Littafi Mai Tsarki › Karin Magana 12:10
Ayar Littafi Mai Tsarki · SRK
Karin Magana 12:10
Mai adalci kan kula da bukatun dabbobinsa, amma halaye mafi kyau na mugaye su ne ƙeta.
Karanta dukan babin: Karin Magana 12
A cikin mahallinsa
7Akan tumɓuke mugaye ba a ƙara ganinsu, amma gidan masu adalci kan tsaya daram.
8Akan yabi mutum bisa ga hikimarsa, amma mutane marasa azanci akan rena su.
9Gara ka zama kai ba kome ba ne amma kana da bawa da ka mai da kanka kai wani ne alhali kuwa ba ka da abinci.
10Mai adalci kan kula da bukatun dabbobinsa, amma halaye mafi kyau na mugaye su ne ƙeta.
11Duk wanda ya nome gonarsa zai sami abinci a yalwace, amma shi da yake naushin iska marar azanci ne.
12Mugaye suna sha’awar ganimar mugayen mutane, amma saiwar masu adalci kan haɓaka.
13Mugun mutum kan fāɗa a tarkon maganarsa ta zunubi, amma adali kan kuɓuta daga wahala.
Da Turanci
A righteous man regards the life of his animal, but the tender mercies of the wicked are only cruelty.Nassoshi masu alaƙa
Sassan da masu karatu suka fi danganta wa da wannan.
Kada ku yi wa saniya takunkumi sa’ad da take tattaka hatsi.Tushe: OpenBible.info, CC BY 4.0 · Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi