Bible Explorer

Gida › Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce › Matsin lamba

Motsin zuciya

Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da Matsin lamba

Ayoyin da masu karatu suka fi komawa gare su don wannan jigo (15), an ambace su gaba ɗaya daga Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa.

Fil 4:6–7Kada ku damu game da kome sai dai a cikin abu duka, ku gabatar da roƙe-roƙenku ga Allah ta wurin addu’a da roƙo, tare da godiya. Salamar Allah, wadda ta wuce dukan fahimta, za tă tsai da zukatanku da tunaninku cikin Kiristi Yesu.
Yoh 14:27Salama na bari tare da ku; salamata nake ba ku. Ba kamar yadda duniya take bayarwa nake ba ku ba. Kada zuciyarku ta ɓaci kada kuma ku ji tsoro.
Mat 11:28–30“Ku zo gare ni, dukanku da kuka gaji kuke kuma fama da kaya, zan kuwa ba ku hutu. Ku ɗauki karkiyata a kanku, ku kuma yi koyi da ni, gama ni mai tawali’u ne marar girman kai, za ku kuwa sami hutu don rayukanku. Gama karkiyata mai sauƙi ce, kayana kuma marasa nauyi ne.”
Rom 8:31Me za mu ce ke nan game da wannan abu? In Allah yana goyon bayanmu, wa kuwa zai iya gāba da mu?
Zab 55:22Ku kawo damuwoyinku ga Ubangiji zai kuwa riƙe ku; ba zai taɓa barin mai adalci yă fāɗi ba.
1Bit 5:7Ku danƙa masa dukan damuwarku, domin shi ne yake lura da ku.
Mat 6:34Saboda haka kada ku damu game da gobe, gama gobe zai damu da kansa. Damuwar yau ma ta isa wahala.
1Yoh 4:18Babu tsoro cikin ƙauna. Cikakkiyar ƙauna dai takan kawar da tsoro, domin hukunci ne yake kawo tsoro. Mai jin tsoro ba cikakke ba ne a cikin ƙauna.
Yoh 16:33“Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin a cikina ku sami salama. A duniyan nan za ku sha wahala. Amma ku yi ƙarfin hali! Na yi nasara a kan duniya.”
K Mag 12:25Zuciya mai damuwa takan naƙasar da mutum, amma maganar alheri kan faranta masa rai.
Zab 118:5–6Cikin azabata na yi kuka ga Ubangiji, ya kuwa amsa ta wurin ’yantar da ni. Ubangiji yana tare da ni; ba zan ji tsoro ba. Me mutum zai yi mini?
Rom 8:28Mun kuma san cewa a cikin dukan abubuwa Allah yana aikata alheri ga waɗanda suke ƙaunarsa, yana waɗanda aka kira bisa ga nufinsa.
Fil 4:13Ina iya yin kome ta wurin wannan wanda yake ba ni ƙarfi.
K Mag 3:5–6Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka kada kuma ka dangana ga ganewarka; cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi, zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe.
Luk 6:48Yana kama da mutumin da ya gina gida, wanda ya haƙa ƙasa da zurfi, sa’an nan ya kafa tushen ginin a kan dutse. Da ambaliyar ruwa ta taso, ƙarfin ruwa kuwa ya buga gidan, wannan bai jijjiga shi ba, domin an yi masa tushen gini na ainihi.

Waɗannan ayoyi ne da masu karatu suka fi komawa a wannan batu — ba koyarwa a kansa ba. Karanta kowanne a cikin surarsa.

Tushe

Ayoyin kowane jigo da tsarinsu: bayanan jigogi na OpenBible.info, bisa ƙuri’un masu karatu: OpenBible.info · CC BY 4.0

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.