Gida › Shahararrun ayoyin Littafi Mai Tsarki › Karin Magana 16:3
Ayar Littafi Mai Tsarki · SRK
Karin Magana 16:3
Ka miƙa wa Ubangiji dukan abin da kake yi, shirye-shiryenka kuwa za su yi nasara.
Karanta dukan babin: Karin Magana 16
A cikin mahallinsa
1Ga mutum ne shirye-shiryen zuciya suke, amma daga Ubangiji ne amshin harshe kan zo.
2Dukan hanyoyin mutum sukan yi kamar marar laifi ne gare shi, amma Ubangiji yakan auna manufofi.
3Ka miƙa wa Ubangiji dukan abin da kake yi, shirye-shiryenka kuwa za su yi nasara.
4Ubangiji yana yin kome domin amfaninsa, har ma da mugaye domin ranar masifa.
5Ubangiji yana ƙyamar dukan zuciya mai girman kai. Ka tabbata da wannan. Ba za su kuɓuta daga hukunci ba.
6Ta wurin ƙauna da aminci akan yi kafarar zunubi; ta wurin tsoron Ubangiji mutum kan guji mugunta.
Da Turanci
Nassoshi masu alaƙa
Sassan da masu karatu suka fi danganta wa da wannan.
Ka ji daɗinka a cikin Ubangiji zai kuwa biya bukatun zuciyarka. Ka sa kanka a hanyar Ubangiji; ka kuma dogara gare shi zai kuwa yi wannan.cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi, zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe.Ku kawo damuwoyinku ga Ubangiji zai kuwa riƙe ku; ba zai taɓa barin mai adalci yă fāɗi ba.Kada ku damu game da kome sai dai a cikin abu duka, ku gabatar da roƙe-roƙenku ga Allah ta wurin addu’a da roƙo, tare da godiya.Ku danƙa masa dukan damuwarku, domin shi ne yake lura da ku.Abin da ka zaɓa za ka yi za ka yi nasara a ciki, haske kuma zai haskaka hanyarka.“Amma da a ce ni ne, da zan roƙi Allah; zan gaya masa damuwata.Sai Yesu ya ce wa almajiransa, “Saboda haka, ina faɗa muku, kada ku damu game da rayuwarku, abin da za ku ci, ko kuma game da jikinku, abin da za ku yafa.Tushe: OpenBible.info, CC BY 4.0 · Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi