Gida › Shahararrun ayoyin Littafi Mai Tsarki › Afisawa 6:4
Ayar Littafi Mai Tsarki · SRK
Afisawa 6:4
Ku kuma iyaye, kada ku tsokane ’ya’yanku. Ku yi musu reno mai kyau. Ku koyar da su, ku kuma gargaɗe su game da Ubangiji.
Karanta dukan babin: Afisawa 6
A cikin mahallinsa
1Ku ’ya’ya, ku yi biyayya ga iyayenku, gama ku na Ubangiji, abin da ya dace ku yi ke nan.
2Doka ta farko wadda aka haɗa da alkawari ita ce, “Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,
3don ka zauna lafiya, ka kuma yi tsawon rai a duniya.”
4Ku kuma iyaye, kada ku tsokane ’ya’yanku. Ku yi musu reno mai kyau. Ku koyar da su, ku kuma gargaɗe su game da Ubangiji.
5Ku bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku na duniya. Ku nuna musu halin bangirma, kuna kuma yin musu biyayya cikin dukan abu, da zuciya ɗaya kamar ga Kiristi kuke yi.
6Ku yi aiki sosai, ba don kawai ku gamshe su sa’ad da suke kallonku ba. Da yake ku bayin Kiristi ne, ku aikata nufin Allah da dukan zuciyarku.
7Ku yi aikinku da kyakkyawar niyya, sai ka ce ga Ubangiji kuke yi, ba mutane ba.
Da Turanci
Fathers, do not provoke your children to wrath; instead, bring them up in the discipline and instruction of the Lord.Nassoshi masu alaƙa
Sassan da masu karatu suka fi danganta wa da wannan.
Ubanni, kada ku matsa wa yaranku lamba, don kada su fid da zuciya.Ka hori yaro a hanyar da ya kamata yă bi, kuma sa’ad da ya tsufa ba zai bar ta ba.Sandar gyara kan ba da hikima, amma yaron da aka bari ba horo kan jawo kunya ga mahaifiyarsa.Ka hori ɗanka, gama yin haka akwai sa zuciya; kada ka goyi baya lalacewarsa.Ku koya wa ’ya’yanku su da himma. Yi musu magana game da su sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya a hanya, sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi.da kuma yadda tun kana ɗan jinjiri ka san Nassosi masu tsarki, waɗanda suke iya sa ka zama mai hikima zuwa ceto ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu.Ka hori ɗanka, zai kuwa ba ka salama; zai ba ka farin cikin da kake so.Kada ka bar yaro ba horo; in ka yi masa horo da sanda, ba zai mutu ba. Ka hukunta shi da sanda ka ceci ransa daga mutuwa.Tushe: OpenBible.info, CC BY 4.0 · Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi