Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Shahararrun ayoyin Littafi Mai Tsarki › Yohanna 4:24

Ayar Littafi Mai Tsarki · SRK

Yohanna 4:24

Allah ruhu ne, masu yi masa sujada kuwa dole su yi masa sujada a ruhu, da gaskiya kuma.”

Karanta dukan babin: Yohanna 4

A cikin mahallinsa

21Sai Yesu ya ce, “Uwargida, ina tabbatar miki, lokaci yana zuwa da ba za ku yi wa Uba sujada ko a dutsen nan, ko kuwa a Urushalima ba.

22Ku Samariyawa ba ku san abin da kuke yi wa sujada ba; mu kuwa mun san abin da muke yi wa sujada, gama ceto daga Yahudawa yake.

23Duk da haka, lokaci yana zuwa har ma ya riga ya yi, da masu sujada na gaskiya za su yi wa Uba sujada a Ruhu da kuma gaskiya, gama irin waɗannan masu sujada ne Uba yake nema.

24Allah ruhu ne, masu yi masa sujada kuwa dole su yi masa sujada a ruhu, da gaskiya kuma.”

25Macen ta ce, “Na san cewa Almasihu” (da ake ce da shi Kiristi) “yana zuwa. Sa’ad da ya zo kuwa, zai bayyana mana kome.”

26Sai Yesu ya ce, “Ni mai maganan nan da ke, Ni ne shi.”

27Suna gama magana ke nan sai almajiransa suka iso, suka yi mamakin ganin yana magana da mace. Amma ba wanda ya ce, “Me kake so?” Ko “Me ya sa kake magana da ita?”

Yohanna 4

Da Turanci

Berean Standard BibleJohn 4:24God is Spirit, and His worshipers must worship Him in spirit and in truth.”

Nassoshi masu alaƙa

Sassan da masu karatu suka fi danganta wa da wannan.

2Kor 3:17Ubangiji fa, shi ne Ruhu, kuma duk inda Ruhun Ubangiji yake, a nan ’yanci yake.
Mat 15:8–9“ ‘Waɗannan mutane da baki kawai suke girmama ni, amma zukatansu suna nesa da ni. A banza suke mini sujada, koyarwarsu, dokoki ne kawai da mutane suke koyarwa.’ ”
Fil 3:3Gama mu ne masu kaciya, mu da muke yi sujada ta wurin Ruhun Allah, mu da muke taƙama a cikin Kiristi Yesu, mu da ba mu dogara da ayyukan da ake gani ba,
Zab 51:17Hadayun Allah su ne karyayyen ruhu; karyayyiya da kuma zuciya mai tuba, Ya Allah, ba za ka ƙi ba.
Ish 57:15Gama abin da Maɗaukaki da kuma Mai daraja ya faɗa wanda yake raye har abada, wanda sunansa mai tsarki ne, “Ina zama a bisa da kuma a tsattsarkan wuri, amma kuma tare da shi wanda yake mai halin tuba mai tawali’u a ruhu, don in farfaɗo da ruhu mai tawali’u in kuma farfaɗo da zuciyar mai halin tuba.
1Sam 16:7Amma Ubangiji ya ce wa Sama’ila, “Kada ka dubi kyan tsarinsa ko tsayinsa, domin ba shi nake so ba, gama yadda Ubangiji yake gani, ba haka mutum yake gani ba. Mutum yakan dubi kyan tsari ne kawai daga waje, amma Ubangiji yakan dubi zuciya.”
1Tim 1:17Bari girma da ɗaukaka su tabbata har abada abadin ga Sarki madawwami, wanda ba ya mutuwa, wanda ba a ganinsa, wanda kuma shi ne kaɗai Allah! Amin.
Zab 66:18Da a ce na ji daɗin zunubi a zuciyata, da Ubangiji ba zai saurara ba;

Tushe: OpenBible.info, CC BY 4.0 · Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi