Gida › Shahararrun ayoyin Littafi Mai Tsarki › Yohanna 1:1
Ayar Littafi Mai Tsarki · SRK
Yohanna 1:1
Tun farar farawa akwai Kalma, Kalman kuwa yana nan tare da Allah, Kalman kuwa Allah ne.
Karanta dukan babin: Yohanna 1
A cikin mahallinsa
1Tun farar farawa akwai Kalma, Kalman kuwa yana nan tare da Allah, Kalman kuwa Allah ne.
2Yana nan tare da Allah tun farar farawa.
3Ta wurin Kalman ne aka halicci dukan abubuwa. In ba tare da shi ba, babu abin da aka yi wanda aka yi.
4A cikinsa rai ya kasance, wannan rai kuwa shi ne hasken mutane.
Da Turanci
In the beginning was the Word, and the Word was with God, and the Word was God.Nassoshi masu alaƙa
Sassan da masu karatu suka fi danganta wa da wannan.
A farko-farko, Allah ya halicci sama da ƙasa.Yanzu ya Uba, ka ɗaukaka ni a gabanka da ɗaukakar da dā nake da ita tun kafin a kafa duniya.Yana saye da rigar da aka tsoma a jini, sunansa kuwa Kalman Allah ne.Ya kasance kafin dukan abu, kuma a cikinsa ne dukan abubuwa suke a harhaɗe.Kalman ya zama mutum, ya kuwa zauna a cikinmu. Muka ga ɗaukakarsa, ɗaukaka ta wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaici, wanda ya zo daga wurin Uba, cike da alheri da gaskiya.Wannan da ya kasance tun farko, wanda muka ji, wanda muka gani da idanunmu, wanda muka duba, hannuwanmu kuma suka taɓa, wannan ne muke shela game da Kalman rai. Wannan Rai ya bayyana, muka kuwa gan shi, muka kuma shaida shi, muna kuwa yin muku shelar wannan rai madawwami, wanda dā yake tare da Uba, ya kuma bayyana a gare mu.Ni ne Alfa da kuma Omega, na Fari da kuma na Baya, Farko da kuma Ƙarshe.Tushe: OpenBible.info, CC BY 4.0 · Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi