Gida › Shahararrun ayoyin Littafi Mai Tsarki › Yohanna 7:24
Ayar Littafi Mai Tsarki · SRK
Yohanna 7:24
Ku daina yin shari’a bisa ga ganin ido, sai dai ku yi shari’a bisa ga adalci.”
Karanta dukan babin: Yohanna 7
A cikin mahallinsa
21Yesu ya ce musu, “Na yi abin banmamaki ɗaya, dukanku kuwa kuka yi mamaki.
22Duk da haka, domin Musa ya bar muku kaciya (ko da yake a gaskiya, ba daga wurin Musa ne ya fito ba, sai dai daga wurin kakannin kakanninku), ga shi kuna yin wa yaro kaciya a ranar Asabbaci.
23To, in za a iya yin wa yaro kaciya a ranar Asabbaci don kada a karya dokar Musa, don me kuke fushi da ni saboda na warkar da mutum a ranar Asabbaci?
24Ku daina yin shari’a bisa ga ganin ido, sai dai ku yi shari’a bisa ga adalci.”
25A nan ne fa waɗansu mutane daga Urushalima suka fara tambaya suna cewa, “Ashe, ba wannan mutum ne suke nema su kashe ba?
26Ga shi nan yana magana a fili, su kuma ba su ce masa uffam ba. Ko hukumomi sun yarda cewa shi ne Kiristi?
27Mun dai san inda mutumin nan ya fito; amma sa’ad da Kiristi ya zo ba wanda zai san inda ya fito.”
Da Turanci
Nassoshi masu alaƙa
Sassan da masu karatu suka fi danganta wa da wannan.
zai kuwa ji daɗin tsoron Ubangiji. Ba zai yi hukunci ta wurin abin da ya gani da idanunsa ba, ba zai kuwa yanke shawara ta wurin abin da ya ji da kunnuwansa ba; amma da adalci zai yi wa masu bukata shari’a, da gaskiya zai yanke shawarwari saboda matalautan duniya. Kamar sanda zai bugi duniya da maganar bakinsa; da numfashin leɓunansa zai yanke mugaye.Amma in kuka nuna bambanci, kun yi zunubi ke nan shari’a kuma ta same ku da laifi a matsayin masu karya doka.Tushe: OpenBible.info, CC BY 4.0 · Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi