Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Shahararrun ayoyin Littafi Mai Tsarki › Afisawa 5:11

Ayar Littafi Mai Tsarki · SRK

Afisawa 5:11

Ku yi nesa da ayyukan duhun da mutane suke yi, a maimakon haka, ku tona su.

Karanta dukan babin: Afisawa 5

A cikin mahallinsa

8Gama a dā zukatanku sun cika da duhu, amma yanzu ku haske ne a cikin Ubangiji. Ku yi rayuwa kamar ’ya’yan haske

9(domin amfanin haske ya ƙunshi nagarta, adalci, da kuma gaskiya)

10ku nemi abin da zai gamshi Ubangiji.

11Ku yi nesa da ayyukan duhun da mutane suke yi, a maimakon haka, ku tona su.

12Gama abin kunya ne a ma faɗi abubuwan da marasa biyayya suke yi a ɓoye.

13Duk abin da aka kawo a gaban haske ana iya ganinsa, kuma duk abin da aka haskaka yakan zama haske.

14Shi ya sa aka ce, “Ka farka, ya kai mai barci, ka tashi daga matattu, Kiristi kuwa zai haskaka ka.”

Afisawa 5

Da Turanci

Berean Standard BibleEphesians 5:11Have no fellowship with the fruitless deeds of darkness, but rather expose them.

Nassoshi masu alaƙa

Sassan da masu karatu suka fi danganta wa da wannan.

Rom 13:12Dare fa ya kusan ƙarewa; gari kuma yana gab da wayewa. Saboda haka bari mu kawar da ayyukan duhu mu kuma yafa kayan yaƙi na haske.
1Tim 5:20Amman waɗannan dattawa waɗanda suke yin zunubi kuwa sai ka kwaɓe su a gaban jama’a, don saura su ji tsoro.
2Tes 3:6A cikin sunan Ubangiji Yesu Kiristi, muna muku umarni, ’yan’uwa, da ku kiyaye kanku daga kowane ɗan’uwa mai zaman banza da ba ya rayuwa bisa ga koyarwar da kuka karɓa daga wurinmu.
2Yoh 1:10–11Duk wanda ya zo wurinku bai kuma kawo koyarwan nan ba, kada ku karɓe shi a gidanku ko ku marabce shi. Duk wanda ya karɓe shi yana tarayya da mugun aikinsa ke nan.
Rom 16:17Ina roƙonku, ’yan’uwa, ku yi hankali fa da masu raba tsakani, saɓanin koyarwar da kuka koya, suna sa tuntuɓe. Ku yi nesa da su.
2Tes 3:14In wani bai yi biyayya da umarninmu a wannan wasiƙa ba, sai fa ku lura da shi. Kada ku haɗa kai da shi, don yă ji kunya.
Zab 1:1–2Mai farin ciki ne mutumin da ba ya aiki da shawarar mugaye ko yă yi abin da masu zunubi suke yi ko yă zauna tare da masu yin ba’a. Amma yana jin daɗin bin dokar Ubangiji, kuma yana ta nazarinta dare da rana.
R Yoh 18:4Sai na ji wata murya daga sama ta ce, “Ku fita daga cikinta, mutanena, don kada zunubanta su shafe ku, don kada wata annobarta ta same ku;

Tushe: OpenBible.info, CC BY 4.0 · Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi