Gida › Shahararrun ayoyin Littafi Mai Tsarki › Yohanna 8:32
Ayar Littafi Mai Tsarki · SRK
Yohanna 8:32
Sa’an nan za ku san gaskiya, gaskiyar kuwa za tă ’yantar da ku.”
Karanta dukan babin: Yohanna 8
A cikin mahallinsa
29Wanda kuwa ya aiko ni yana tare da ni; bai bar ni ni kaɗai ba, domin kullum ina aikata abin da ya gamshe shi.”
30Sa’ad da yake cikin magana, da yawa suka ba da gaskiya gare shi.
31Sai Yesu ya ce wa Yahudawan da suka gaskata da shi, “In dai kun riƙe koyarwata, ku almajiraina ne da gaske.
32Sa’an nan za ku san gaskiya, gaskiyar kuwa za tă ’yantar da ku.”
33Sai suka amsa masa suka ce, “Ai, mu zuriyar Ibrahim ne kuma ba mu taɓa bauta wa kowa ba. Yaya za ka ce za a ’yantar da mu?”
34Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, duk mai yin zunubi bawan zunubi ne.
35Bawa dai ba shi da wurin zama na ɗinɗinɗin a cikin iyali, amma ɗa na gida ne har abada.
Da Turanci
Nassoshi masu alaƙa
Sassan da masu karatu suka fi danganta wa da wannan.
gama ta wurin Kiristi Yesu dokar Ruhu mai ba da rai ta ’yantar da ni daga Dokar Musa.Saboda haka in Ɗan ya ’yantar da ku, za ku ’yantu da gaske.Ka tsarkake su ta wurin gaskiya; maganarka ce gaskiya.Ku yi rayuwa kamar mutanen da aka ’yantar, sai dai kada ku yi amfani da ’yancinku a matsayin hujjar aikata mugunta; ku yi rayuwa kamar bayin Allah.Yesu ya amsa ya ce, “Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai dai ta wurina.Amma a yanzu da aka ’yantar da ku daga zunubi kuka kuma zama bayi ga Allah, ribar da kuka samu tana kai ga zaman tsarki, ƙarshenta kuwa rai madawwami ne.Gama zunubi ba zai zama maigidanku ba, domin ba kwa ƙarƙashin doka, sai dai ƙarƙashin alheri. Me za mu ce ke nan? Za mu ci gaba yin zunubi domin ba ma ƙarƙashin doka sai dai ƙarƙashin alheri? Sam, ko kaɗan! Ba ku sani ba cewa sa’ad da kuka miƙa kanku ga wani don ku yi masa biyayya a matsayin bayi, ko ku bayi ne ga zunubi, wanda yake kai ga mutuwa, ko kuwa ga biyayya, wadda take kai ga adalci, ashe, ba kun zama bayi ga wannan da kuke yi wa biyayya ba ke nan? Amma godiya ga Allah don ko da yake a dā ku bayi ne ga ikon zunubi, da dukan zuciyarku kun yi biyayya ga irin koyarwar da aka danƙa muku. An ’yanta ku daga zunubi, kun kuma zama bayi ga aikin adalci.Ruhun Ubangiji Mai Iko Duka yana a kaina, domin Ubangiji ya shafe ni domin in yi wa’azi labari mai daɗi ga matalauta. Ya aiko ni in warkar da waɗanda suka karai a zuci, don in yi shelar ’yanci don ɗaurarru in kuma kunce ’yan kurkuku daga duhuTushe: OpenBible.info, CC BY 4.0 · Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi