Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Shahararrun ayoyin Littafi Mai Tsarki › Karin Magana 29:11

Ayar Littafi Mai Tsarki · SRK

Karin Magana 29:11

Wawa yakan nuna fushinsa a fili, amma mai hikima kan kanne fushinsa.

Karanta dukan babin: Karin Magana 29

A cikin mahallinsa

8Masu ba’a kan kuta faɗa a birni, amma masu hikima sukan kwantar da fushi.

9In mai hikima ya je wurin shari’a da wawa, wawa kan yi ta fushi yana ta dariya, ba kuwa za a sami salama ba.

10Masu kisankai sukan ƙi mutum mai mutunci su kuma nema su kashe mai aikata gaskiya.

11Wawa yakan nuna fushinsa a fili, amma mai hikima kan kanne fushinsa.

12In mai mulki yana sauraran ƙarairayi, dukan ma’aikatansa za su zama mugaye.

13Matalauci da azzalumi suna da wannan abu ɗaya. Ubangiji ne yake ba dukansu gani.

14In sarki yana hukunta talakawa da adalci kursiyinsa kullum zai kasance lafiya.

Karin Magana 29

Da Turanci

Berean Standard BibleProverbs 29:11A fool vents all his anger, but a wise man holds it back.

Nassoshi masu alaƙa

Sassan da masu karatu suka fi danganta wa da wannan.

K Mag 19:11Hikimar mutum kan ba shi haƙuri; ɗaukakarsa ce ya ƙyale laifi.
K Mag 12:16Wawa kan nuna fushinsa nan take, amma mai la’akari kan ƙyale zargi.
Mik 7:5Kada ka yarda da maƙwabci; kada ka sa begenka ga abokai. Ko ma wadda take kwance a ƙirjinka, ka yi hankali da kalmominka.

Tushe: OpenBible.info, CC BY 4.0 · Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi