Bible Explorer

Bincika › Littattafan Bishara gefe da gefe › A Galili

Littattafan Bishara gefe da gefe · A Galili

Ciyar da mutum dubu huɗu

Mat 15:32–39 · Mar 8:1–10

Mattiyu

Mat 15:32–39

32Yesu ya kira almajiransa wurinsa ya ce, “Ina jin tausayin mutanen nan; gama kwana uku ke nan suke tare da ni ba abin da za su ci. Ba na so in sallame su da yunwa, don kada su kāsa a hanya.”

33Sai almajiransa suka amsa suka ce, “Ina za mu sami isashen burodi a wannan wurin da babu kowa mu ciyar da irin taron nan?”

34Yesu ya tambaye su, “Burodi guda nawa kuke da shi?” Suka amsa suka ce, “Guda bakwai da ’yan ƙananan kifaye.”

35Ya sa taron su zazzauna a ƙasa.

36Sa’an nan ya ɗauki burodi guda bakwai da kuma kifayen nan, da ya yi godiya, sai ya kakkarya su ya ba wa almajiran, su kuma suka ba wa mutane.

37Duk kuwa suka ci, suka ƙoshi. Daga baya almajiran suka kwashe ragowar gutsattsarin cike da kwanduna bakwai.

38Yawan waɗanda suka ci kuwa, maza dubu huɗu ne, ban da mata da yara.

39Bayan Yesu ya sallami taron, sai ya shiga jirgin ruwa ya tafi wajajen Magadan.

Markus

Mar 8:1–10

1A kwanakin nan wani taro mai girma ya taru. Tun da yake ba su da abin da za su ci, sai Yesu ya kira almajiransa ya ce,

2“Ina jin tausayin mutanen nan, kwanansu uku ke nan tare da ni, kuma ba su da abin da za su ci.

3In na sallame su gida da yunwa, za su kāsa a hanya, don waɗansu daga cikinsu sun zo daga nesa.”

4Almajiransa suka amsa suka ce, “Amma a ina, a wannan wurin da ba kowa, wani zai iya samun isashen burodi, don a ciyar da su?”

5Sai Yesu ya yi tambaya ya ce, “Burodi guda nawa kuke da su?” Suka ce, “Bakwai.”

6Sai ya gaya wa taron su zazzauna a ƙasa. Bayan ya ɗauki burodin nan bakwai, ya yi godiya, sai ya kakkarya, ya ba wa almajiransa su rarraba wa mutanen, suka kuwa yi haka.

7Suna kuma da ƙananan kifaye kaɗan, ya ba da godiya dominsu, ya kuma ce wa almajiran su rarraba musu.

8Mutanen suka ci, suka ƙoshi. Daga baya, almajiran suka tattara gutsattsarin da suka rage cike da kwanduna bakwai.

9Wajen maza dubu huɗu ne suka kasance. Da ya sallame su,

10sai ya shiga jirgin ruwa tare da almajiransa, suka tafi yankin Dalmanuta.

An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY