Bible Explorer

Bincika › Littattafan Bishara gefe da gefe › A Galili

Littattafan Bishara gefe da gefe · A Galili

Bangaskiyar mutuniyar Kan’ana

Mat 15:21–28 · Mar 7:24–30

Mattiyu

Mat 15:21–28

21Barin wurin ke nan, sai Yesu ya janye zuwa yankin Taya da Sidon.

22Wata mutuniyar Kan’ana daga wajajen ta zo wurinsa, tana ihu tana cewa, “Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai! ’Yata tana shan wahala ƙwarai daga aljanin da yake cikinta.”

23Yesu bai ce mata uffam ba. Saboda haka almajiransa suka zo wurinsa suka roƙe shi suka ce, “Ka kore ta tă tafi, tana ta binmu tana damunmu da ihu.”

24Ya amsa ya ce, “An aiko ni wurin ɓatattun tumakin Isra’ila ne kaɗai.”

25Sai macen ta zo ta durƙusa a gabansa ta ce, “Ubangiji, ka taimake ni!”

26Ya amsa ya ce, “Ba daidai ba ne a ɗauki abincin yara a jefa wa karnukansu.”

27Ta amsa, ta ce, “I, Ubangiji, amma karnuka ma sukan ci gutsattsarin da sukan fāɗi daga teburin maigidansu.”

28Sa’an nan Yesu ya amsa ya ce, “Mace, kina da bangaskiya mai yawa! An biya miki bukatarki.” ’Yarta kuwa ta warke nan take.

Markus

Mar 7:24–30

24Sai Yesu ya bar wurin, ya kuma tafi wajajen Taya. Ya shiga wani gida, bai kuwa so kowa yă sani ba. Duk da haka, bai iya ɓoye kasancewarsa ba.

25Da jin labarinsa, sai wata mace wadda ƙaramar diyarta tana da mugun ruhu, ta zo ta durƙusa a gabansa.

26Macen kuwa mutuniyar Hellenawa ce, an haife ta a Funisiya a Suriya. Ta roƙi Yesu yă fitar da aljani da yake jikin diyarta.

27Yesu ya ce mata, “Da farko, bari ’ya’ya su ci su ƙoshi tukuna, gama ba daidai ba ne, a ɗauki burodin yara a jefa wa karnukansu.”

28Ta amsa, ta ce, “I, Ubangiji, ko karnuka ma da suke ƙarƙashin tebur, sukan ci burbuɗin da suke fāɗuwa daga abincin yara.”

29Sai ya ce mata, “Saboda irin wannan amsa, ki tafi, aljanin ya rabu da diyarki.”

30Ta tafi gida, ta tarar da diyarta kwance a gado, aljanin kuwa ya fita.

An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY