Bible Explorer

Bincika › Littattafan Bishara gefe da gefe › A Galili

Littattafan Bishara gefe da gefe · A Galili

Neman alama; yistin Farisiyawa

Mat 16:1–12 · Mar 8:11–21

Mattiyu

Mat 16:1–12

1Farisiyawa da Sadukiyawa suka zo don su gwada Yesu ta wurin neman yă nuna musu wata alama daga sama.

2Ya amsa ya ce, “Sa’ad da yamma ta yi, kukan ce, ‘Yanayi zai yi kyau, gama sararin sama ya yi ja,’

3da safe kuma, ku ce, ‘Yau kam za a yi hadari, gama sararin sama ya yi ja, ya kuma ɓata fuska.’ Kun san yadda za ku fassara yanayin sararin sama, amma ba kwa iya fassarar alamun lokuta.

4Wannan mugu da mazinacin zamani yana neman wani abin banmamaki, amma ba wata alamar da za a nuna wa wannan zamani sai dai ta Yunana.” Sai Yesu ya bar su ya tafi abinsa.

5Da suka ƙetare tafkin, almajiran sun manta su riƙe burodi.

6Yesu ya ce musu, “Ku yi hankali, ku yi taka zallan da yistin Farisiyawa da Sadukiyawa.”

7Sai suka fara tattaunawa da junansu suna cewa, “Ko don ba mu kawo burodi ba ne.”

8Sane da abin da suke zance, sai Yesu ya ce, “Ku masu ƙarancin bangaskiya, don me kuke magana da junanku a kan ba ku zo da burodi ba?

9Har yanzu ba ku gane ba ne? Ba ku tuna da gurasa biyar ɗin nan na mutum dubu biyar ba? Kwando nawa kuka tattara cike?

10Ko kuma burodi bakwai nan na mutum dubu huɗu, cikakku manyan kwanduna nawa kuka ɗauka?

11Yaya kuka kāsa gane cewa ba zancen burodi nake yi ba? Sai dai ku yi hankali da yistin Farisiyawa da Sadukiyawa.”

12Sa’an nan suka gane ba cewa yake musu su yi hankali da yistin da ake amfani da shi a burodi ba ne, sai dai su yi hankali da koyarwar Farisiyawa da Sadukiyawa ne.

Markus

Mar 8:11–21

11Farisiyawa suka zo suka fara yin wa Yesu tambayoyi. Don su gwada shi, sai suka nemi yă nuna musu wata alama daga sama.

12Sai ya ja numfashi mai zurfi ya ce, “Don me wannan zamani yake neman ganin abin banmamaki? Gaskiya nake gaya muku, ba wata alamar da za a ba su.”

13Sai ya bar su, ya koma cikin jirgin ruwan, suka ƙetare zuwa ɗaya hayin.

14Almajiran suka manta su riƙe burodi, sai dai guda ɗaya da suke da shi a cikin jirgin ruwan.

15Yesu ya gargaɗe su ya ce, “Ku yi hankali, ku kuma lura da yistin Farisiyawa da na Hiridus.”

16Suka tattauna wannan da juna, suna cewa, “Don ba mu da burodi ne.”

17Da ya gane abin da suke tattaunawa, sai Yesu ya tambaye su ya ce, “Don me kuke zancen rashin burodi? Har yanzu ba ku gane ko fahimta ba? Zukatanku sun taurare ne?

18Kuna da idanu, amma kun kāsa gani, kuna da kunnuwa, amma kun kāsa ji? Ba ku tuna ba?

19Da na kakkarya burodi guda biyar wa mutane dubu biyar, kwanduna nawa kuka kwashe cike da gutsattsarin?” Suka amsa, “Sha biyu.”

20“Da na kuma kakkarya burodin nan bakwai wa mutum dubu huɗu, kwanduna nawa kuka kwashe cike da gutsattsarin?” Suka ce, “Bakwai.”

21Ya ce musu, “Har yanzu ba ku fahimta ba?”

An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY