Gida › Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce › Farin ciki
Motsin zuciya
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da Farin ciki
Ayoyin da masu karatu suka fi komawa gare su don wannan jigo (14), an ambace su gaba ɗaya daga Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa.
Fil 4:4
Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji kullum. Ina sāke gaya muku ku yi farin ciki!Zab 144:15
Masu albarka ne mutanen da wannan zai zama haka; masu albarka ne mutanen da Allah ne Ubangiji.K Mag 15:13
Zuciya mai farin ciki kan sa fuska tă yi haske, amma ciwon zuciya kan ragargaza rai.K Mag 17:22
Zuciya mai farin ciki magani ne mai kyau, amma bakin rai kan busar da ƙasusuwa.Zab 37:4
Ka ji daɗinka a cikin Ubangiji zai kuwa biya bukatun zuciyarka.M Had 3:12–13
Na san ba abin da ya fi wa mutane kyau fiye da su ji daɗi su kuma yi alheri yayinda suke da rai. Cewa kowa yă ci, yă sha, yă kuma ji daɗi cikin dukan aikinsa, wannan kyautar Allah ce.Rom 15:13
Bari Allah na bege yă cika ku da matuƙar farin ciki da salama yayinda kuke dogara gare shi, domin ku yalwata cikin bege ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.Rom 12:12
Ku yi farin ciki cikin bege, haƙuri cikin shan wuya, aminci cikin addu’a.Zab 16:11
Ka sanar da ni hanyar rai; za ka cika ni da farin ciki a gabanka, da madawwamin jin daɗi a hannun damarka.Yoh 16:24
Har yanzu dai ba ku roƙi kome cikin sunana ba. Ku roƙa za ku kuwa samu, farin cikinku kuwa zai zama cikakke.Gal 5:22–23
Amma amfanin da Ruhu yake bayar shi ne ƙauna, farin ciki, salama, haƙuri, kirki, nagarta, aminci, sauƙinkai, da kuma kamunkai. Ai, ba ruwan Doka da waɗannan abubuwa.Zab 34:8
Ku gwada ku gani cewa Ubangiji yana da kyau; mai albarka ne mutumin da yake neman mafaka a gare shi.Ish 26:3–4
Za ka kiyaye shi da cikakken salama shi wanda ya kafa zuciyarsa gare ka, domin ya dogara a gare ka. Ku dogara ga Ubangiji, gama shi Ubangiji, ne madawwamin Dutse.Irm 29:11
Gama na san shirye-shiryen da na yi muku,” in ji Ubangiji, “shirye-shiryen cin gaba ba na cutarwa ba, shirye-shiryen ba ku sa zuciya da kuma na nan gaba.Waɗannan ayoyi ne da masu karatu suka fi komawa a wannan batu — ba koyarwa a kansa ba. Karanta kowanne a cikin surarsa.
Tushe
Ayoyin kowane jigo da tsarinsu: bayanan jigogi na OpenBible.info, bisa ƙuri’un masu karatu: OpenBible.info · CC BY 4.0
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.