Gida › Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce › Littafi Mai Tsarki
Bangaskiya
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da Littafi Mai Tsarki
Ayoyin da masu karatu suka fi komawa gare su don wannan jigo (15), an ambace su gaba ɗaya daga Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa.
2Tim 3:16
Dukan Nassi numfashin Allah ne yana kuma da amfani don koyarwa, tsawatarwa, gyara da kuma horarwa cikin adalci,Ibr 4:12
Maganar Allah tana da rai, tana kuma da ƙarfin aiki. Ta fi kowane takobi mai baki biyu kaifi. Maganarsa takan ratsa har ciki-ciki, tana raba rai da ruhu, gaɓoɓi da kuma ɓargon ƙashi; har sai ta tone ainihi wane ne muke.Rom 15:4
Gama duk abin da aka rubuta a dā an rubuta ne domin yă koya mana, don ta wurin jimrewa da kuma ƙarfafawar Nassosi mu kasance da bege.Zab 119:105
Maganarka fitila ce ga ƙafafuna haske kuma a kan hanyata.Mat 4:4
Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake cewa, ‘Ba da abinci kaɗai mutum yake rayuwa ba, sai dai da kowace kalmar da take fitowa daga bakin Allah.’ ”Yosh 1:8
Kada ka bar Littafin Dokokin nan yă rabu da bakinka, sai dai ka yi ta tunani game da shi dare da rana, don ka lura, ka yi duk abin da aka rubuta a ciki, ta haka ne za ka yi nasara cikin duk abin da za ka yi.Zab 119:11
Na ɓoye maganarka a cikin zuciyata don kada in yi maka zunubi.Zab 119:18
Ka buɗe idanuna don in iya gani abubuwan banmamaki a cikin dokarka.1Bit 2:2
Kamar sababbin jarirai, ku yi marmarin madara zalla ta ruhaniya, domin ta wurinta za ku yi girma cikin cetonku,K Mag 30:5
“Kowace maganar Allah ba ta da kuskure; shi ne garkuwa ga waɗanda suke neman mafaka daga gare shi.Yoh 17:17
Ka tsarkake su ta wurin gaskiya; maganarka ce gaskiya.Ayu 23:12
Ban fasa bin dokokin da ya bayar ba; na riƙe maganarsa da muhimmanci fiye da abincin yau da gobe.Ish 55:11
haka maganata da take fitowa daga bakina. Ba za tă koma gare ni wofi ba, amma za tă cika abin da nake so ta kuma cika abin da na aike ta tă yi.Mar 13:31
Sama da ƙasa za su shuɗe, amma kalmomina ba za su taɓa shuɗewa ba.Rom 10:17
Saboda haka, bangaskiya takan zo ne ta wurin jin saƙo, akan ji saƙon kuma ta wurin maganar Kiristi.Waɗannan ayoyi ne da masu karatu suka fi komawa a wannan batu — ba koyarwa a kansa ba. Karanta kowanne a cikin surarsa.
Tushe
Ayoyin kowane jigo da tsarinsu: bayanan jigogi na OpenBible.info, bisa ƙuri’un masu karatu: OpenBible.info · CC BY 4.0
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.