Bible Explorer

Bincika › Littattafan Bishara gefe da gefe › A Urushalima

Littattafan Bishara gefe da gefe · A Urushalima

Ɗan wane ne Kiristi?

Mat 22:41–46 · Mar 12:35–37 · Luk 20:41–44

Mattiyu

Mat 22:41–46

41Yayinda Farisiyawa suke a tattare wuri ɗaya, sai Yesu ya tambaye su,

42“Me kuke tsammani game da Kiristi? Ɗan wane ne shi?” Suka amsa suka ce, “Ɗan Dawuda.”

43Ya ce musu, “To, ta yaya Dawuda ya yi magana ta wurin Ruhu Mai Tsarki, ya kira shi ‘Ubangiji’? Gama ya ce,

44“ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina, “Zauna a hannun damana, sai na sa abokan gābanka su zama matashin sawunka.” ’

45To, in Dawuda ya kira shi ‘Ubangiji,’ yaya zai zama ɗansa?”

46Ba wanda ya iya tanka masa, daga wannan rana kuwa ba wanda ya sāke yin karambanin yin masa wata tambaya.

Markus

Mar 12:35–37

35Yayinda Yesu yake koyarwa a filin haikalin, sai ya yi tambaya ya ce, “Yaya malaman dokoki suke cewa Kiristi ɗan Dawuda ne?

36Dawuda da kansa ya yi magana ta wurin Ruhu Mai Tsarki ya ce, “ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina, “Zauna a hannun damana sai na sa abokan gābanka a ƙarƙashin sawunka.” ’

37Dawuda da kansa ya kira shi ‘Ubangiji.’ To, ta yaya zai zama ɗansa?” Taro mai yawa suka saurare shi da murna.

Luka

Luk 20:41–44

41Sai Yesu ya ce musu, “Yaya suke cewa, ‘Kiristi ɗan Dawuda ne?’

42Dawuda da kansa ya faɗa a cikin Zabura, “ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina, “Zauna a hannun damana,

43sai na sa abokan gābanka su zama matashin sawunka.” ’

44Dawuda ya kira shi ‘Ubangiji.’ Ta, yaya zai zama ɗansa?”

An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY