34Da jin Yesu ya ƙure Sadukiyawa, sai Farisiyawa suka tattaru.
35Ɗaya daga cikinsu, wani masanin Doka, ya gwada shi da wannan tambaya.
36“Malam, wace doka ce mafi girma a cikin dokoki?”
37Yesu ya amsa ya ce, “ ‘Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka da dukan ranka da kuma dukan hankalinka.’
38Wannan, ita ce doka ta fari da kuma mafi girma.
39Ta biye kuma kamar ta farkon take. ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’
40Dukan Doka da Annabawa suna rataya ne a kan waɗannan dokoki biyu.”