Wata gobara ta ci kwanaki ta kuma hallaka yawancin birnin. Masanin tarihi Tacitus ya rubuta cewa Nero ya ɗora wa Kiristoci laifi ya kuma sa aka kashe da yawa daga cikinsu — tsanantawa ta farko da aka sani da Roma ta yi wa Kiristoci.
Kundin sani › A wancan lokaci a duniya
A cikin Littafi Mai Tsarki · kimanin 60–62 B.H. · Roma
Bulus a Roma
Bayan jirginsu ya farfashe a Malta Bulus ya isa Roma, inda ya zauna shekara biyu a ƙarƙashin tsaro, yana karɓar baƙi.
Bayan wata uku sai muka tashi a wani jirgin ruwan da ya ci damina a tsibirin. Jirgin ruwa kuwa na Alekzandariya ne yana da siffar tagwayen allolin Kasto da Follus. Muka isa Sirakus a can muka yi kwana uku. Daga can muka tashi muka isa Regiyum. Kashegari iskar kudu ta taso, kashegari kuma muka kai Futeyoli. A can muka tarar da waɗansu ’yan’uwa waɗanda suka gayyaci mu mu yi mako ɗaya da su. Da haka dai muka kai Roma. ’Yan’uwan da suke can sun sami labari cewa muna zuwa, sai suka tashi tun daga Kasuwar Affiyus da Masauƙi Uku don su tarye mu. Da ganin mutanen nan sai Bulus ya gode wa Allah ya kuma sami ƙarfafawa. Da muka isa Roma, sai aka yarda wa Bulus yă zauna shi kaɗai, tare da sojan da zai yi gadinsa. Bayan kwana uku sai ya kira taron shugabannin Yahudawa. Da suka taru, Bulus ya ce musu, “’Yan’uwana, ko da yake ban yi wa mutanenmu wani laifi ba ko kuma wani abu game da al’adun kakanninmu, aka kama ni a Urushalima aka kuma ba da ni ga Romawa. Suka tuhume ni suka kuma so su sake ni, domin ba a same ni da wani laifin da ya cancanci kisa ba. Amma da Yahudawa suka ƙi, sai ya zama mini dole in ɗaukaka ƙara zuwa gaban Kaisar ba don ina da wani zargin da zan kawo game da mutanena ba. Saboda wannan ne na nemi in gan ku in kuma yi magana da ku. Saboda begen Isra’ila ne, nake a daure da wannan sarƙa.” Suka amsa cewa, “Ba mu sami wani wasiƙa daga Yahudiya game da kai ba, kuma ba kowa daga cikin ’yan’uwan da suka zo daga can ya kawo wani labari ko ya faɗi wani mummuna abu game da kai. Amma muna so mu ji ra’ayinka, gama mun san cewa mutane ko’ina suna muguwar magana a kan wannan ɗarikar.” Suka shirya su sadu da Bulus wata rana, suka ma zo da yawa fiye da dā a wurin da Bulus yake zama. Daga safe har zuwa yamma ya yi ta yin musu bayani, ya kuma shaida musu mulkin Allah yana ƙoƙarin rinjayarsu game da Yesu daga Dokar Musa da kuma daga Annabawa. Waɗansu suka rinjayu da abin da ya faɗa, amma waɗansu suka ba su gaskata ba. Suka kāsa yarda da juna suka fara watsewa bayan Bulus ya yi wannan magana guda cewa, “Ruhu Mai Tsarki ya faɗa wa kakannin-kakanninku gaskiya sa’ad da ya ce ta bakin annabi Ishaya cewa, “ ‘Je ka wurin mutanen nan ka ce, “Za ku yi ta ji amma ba za ku fahimta ba; za ku yi ta dubawa, amma ba za ku gani ba.” Gama zuciyar mutanen nan ta yi tauri; da ƙyar suke ji da kunnuwansu, sun kuma rufe idanunsu. In ba haka ba za su iya gani da idanunsu, su ji da kunnuwansu, su fahimta a zukatansu, su kuma juyo, in kuwa warkar da su.’ “Saboda haka na so ku san cewa an aika da ceton Allah ga Al’ummai, za su kuwa saurara!” Shekaru biyu cif Bulus ya zauna a can a gidansa na haya yana marabtar duk wanda ya je wurinsa. Ya yi wa’azin mulkin Allah yana kuma koyarwa game da Ubangiji Yesu Kiristi, gabagadi ba tare da wani abu ya hana shi ba.A lokaci ɗaya a duniya
Ayyukan Manzanni ya ƙare da Bulus a tsare a Roma shekara biyu, kimanin 60–62 B.H., yana koyarwa a fili a gidan haya (Ayyukan Manzanni 28:30–31). Sarkin shi ne Nero. Ga duniyar shekarun 60 B.H.
A Biritaniya, Sarauniya Boudica ta Iceni ta jagoranci babban tawaye ta kuma ƙone Londinium — sabon garin Romawa da ya zama London — kafin Romawa su ci ta.
A Alexandriya injiniya Hero ya kwatanta ƙwallon da tururi yake juyawa da injunan da iska da ruwa suke aiki da su. Yawanci ana sa shi a zamani ta wurin kusufin wata da ya ambata, wanda ya dace da wani a 62 B.H.
Bisa ga al’adar Sin, sarkin Han Ming ya yi mafarkin wata siffar zinariya ya kuma aika da jakadu zuwa yamma. Sun dawo da sufaye da littattafan Buddha, aka kuma gina musu Haikalin Farin Doki a Luoyang — haikalin Buddha na farko a Sin.
Sarakunan Kushan daga Tsakiyar Asiya sun gina daula a ƙasashen Afghanistan, Pakistan da arewacin Indiya na yau. Ƙasashensu suna kan hanyoyin da suka haɗa Roma, Indiya da Sin.
Tarihin Farko na Kyiv, da aka tattara kimanin 1110, ya ba da labari cewa manzo Andarawus ya yi tafiya a jirgin ruwa a kan Dnieper zuwa sama, ya kafa giciye a kan tuddan da Kyiv za ta tsaya a kai, ya kuma faɗi cewa babban birni zai kasance a can. Masana tarihi suna ganin wannan tatsuniya ce; wata tsohuwar al’ada ta ce Scythia ce filin aikin Andarawus.