Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Shahararrun ayoyin Littafi Mai Tsarki › 2 Korintiyawa 6:14

Ayar Littafi Mai Tsarki · SRK

2 Korintiyawa 6:14

Kada ku haɗa kai da marasa bi. Gama me ya haɗa adalci da mugunta? Ko kuwa me ya haɗa haske da duhu?

Karanta dukan babin: 2 Korintiyawa 6

A cikin mahallinsa

11Ya ku Korintiyawa, mun yi muku magana a sake, muka kuma saki zuciya da ku ƙwarai.

12Ba mu ƙi nuna muku ƙaunarmu ba, sai dai ku kuka ƙi nuna mana.

13A wannan zance kam, ina magana da ku kamar ’ya’yana, ku ma ku saki zuciya da mu.

14Kada ku haɗa kai da marasa bi. Gama me ya haɗa adalci da mugunta? Ko kuwa me ya haɗa haske da duhu?

15Wace daidaituwa ce tsakanin Kiristi da Iblis? Me ya haɗa mai bi da marar bi?

16Wane alkawari ne tsakanin haikalin Allah da na gumaka? Gama mu haikalin Allah mai rai ne. Kamar yadda Allah ya ce, “Zan zauna tare da su, in yi tafiya a cikinsu, zan zama Allahnsu, su kuma za su zama mutanena.”

17Saboda haka, “Sai ku fito daga cikinsu, ku keɓe kanku, in ji Ubangiji. Kada ku taɓa wani abu marar tsabta, zan kuma karɓe ku.”

2 Korintiyawa 6

Da Turanci

Berean Standard Bible2 Corinthians 6:14Do not be unequally yoked with unbelievers. For what partnership can righteousness have with wickedness? Or what fellowship does light have with darkness?

Nassoshi masu alaƙa

Sassan da masu karatu suka fi danganta wa da wannan.

1Kor 15:33Kada fa a ruɗe ku, “Ajiyar mugayen abokai yana ɓata hali mai kyau.”
1Kor 10:21Ba zai yiwu ku sha daga kwaf na Ubangiji ku kuma sha daga kwaf na aljanu ba, ba ya yiwuwa ku ci a teburin Ubangiji, ku kuma ci a teburin aljanu.
Yaƙ 4:4Ku mazinata, ba ku san cewa abokantaka da duniya gāba ce da Allah ba? Duk wanda ya zaɓa yă zama abokin duniya ya zama abokin gāban Allah ke nan.
Fir 19:19“ ‘Ku kiyaye farillaina. “ ‘Kada ku sa dabbobin da ba iri ɗaya ba su yi barbara. “ ‘Kada ku yi shuki iri biyu a gonarku. “ ‘Kada ku sa rigar da aka saƙa da yadi iri biyu.
1Bit 2:9–10Amma ku zaɓaɓɓu ne, ƙungiyar firistocin babban Sarki, al’umma mai tsarki, jama’a mallakar Allah, domin ku shaida yabon shi wanda ya kira ku daga cikin duhu zuwa haskensa mai banmamaki. Dā ku ba mutane ba ne, amma yanzu ku mutanen Allah ne; Dā ba ku karɓi jinƙai ba, amma yanzu kun karɓi jinƙai.
Zab 26:4–5Ba na zama tare da masu ruɗu, ko in yi tarayya da masu riya; na ƙi jinin taron masu aikata mugunta na ƙi in zauna tare da mugaye.
M Sh 22:9–11Kada ku shuka iri biyu a gonar inabinku; in kuka yi haka, ba abin da kuka shuka ne kaɗai zai ƙazantu ba, amma har da inabinku ma. Kada ku haɗa bijimi da jaki su yi noma tare. Kada ku sa rigar ulu da aka gauraye da lilin aka saƙa.
Zab 139:21–22Ba ina ƙin masu ƙinka ba, ya Ubangiji, ina kuma ƙyamar waɗanda suke tayar maka ba? Ba ni da wani abu da nake musu sai kiyaye kawai; na ɗauke su abokan gābana.

Tushe: OpenBible.info, CC BY 4.0 · Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi