Gida › Shahararrun ayoyin Littafi Mai Tsarki › 1 Korintiyawa 10:13
Ayar Littafi Mai Tsarki · SRK
1 Korintiyawa 10:13
Ba jarrabar da ta taɓa samunku, wadda ba a saba yi wa mutum ba. Allah mai aminci ne; ba zai bari a jarrabce ku fiye da ƙarfinku ba. Amma in aka jarrabce ku, zai nuna muku mafita, domin ku iya cin nasara.
Karanta dukan babin: 1 Korintiyawa 10
A cikin mahallinsa
10Kada kuma ku yi gunaguni yadda waɗansunsu suka yi, har mala’ika mai hallakarwa ya hallaka su.
11Waɗannnan abubuwa sun same su ne, domin su zama abubuwan koyi, aka kuma rubuta su domin a gargaɗe mu, mu da ƙarshen zamani ya zo mana.
12Saboda haka in kana tsammani kana tsaye ne, to, ka yi hankali kada ka fāɗi!
13Ba jarrabar da ta taɓa samunku, wadda ba a saba yi wa mutum ba. Allah mai aminci ne; ba zai bari a jarrabce ku fiye da ƙarfinku ba. Amma in aka jarrabce ku, zai nuna muku mafita, domin ku iya cin nasara.
14Saboda haka abokaina ƙaunatattu, ku guje wa bautar gumaka.
15Ina magana da ku a kan ku mutane ne fa masu azanci; ku duba da kanku ku ga abin da nake faɗa.
16Kwaf nan na godiya da muke yin godiya da shi, ashe ba tarayya ce a cikin jinin Kiristi ba? Wannan burodi kuma da muke karya mu ci, ashe, ba tarayya ne a cikin jikin Kiristi ba?
Da Turanci
No temptation has seized you except what is common to man. And God is faithful; He will not let you be tempted beyond what you can bear. But when you are tempted, He will also provide an escape, so that you can stand up under it.Nassoshi masu alaƙa
Sassan da masu karatu suka fi danganta wa da wannan.
in haka ne, to, Ubangiji ya san yadda zai ceci mutane masu tsoron Allah daga gwaje-gwaje, yă kuma tsare marasa adalci don ranar hukunci, har yă zuwa ranar shari’a.Ubangiji zai cece ni daga kowane mugun hari yă kuma kai ni mulkinsa na sama lafiya. A gare shi ɗaukaka ta tabbata har abada abadin. Amin.Ubangiji mai aminci ne, zai ƙarfafa ku, yă kuma tsare ku daga mugun nan.Ku zama masu kamunkai, ku kuma zauna a faɗake. Abokin gābanku, Iblis yana kewayewa kamar zaki mai ruri, yana neman wanda zai cinye. Ku yi tsayayya da shi, kuna tsayawa daram cikin bangaskiya, domin kun san cewa ’yan’uwanku ko’ina a duniya suna shan irin wahalolin nan.Cikin famanku da zunubi, ba ku yi tsayayya har ga zub da jininku ba tukuna.Wannan wanda ya kira ku mai aminci ne zai kuwa aikata.Sau uku na roƙi Ubangiji yă raba ni da wannan abu. Amma ya ce mini, “Alherina ya ishe ka, domin a cikin rashin ƙarfi ne ake ganin cikar ikona.” Saboda haka, zan ƙara yin taƙama da farin ciki game da rashin ƙarfina, domin ikon Yesu Kiristi yă zauna tare da ni. Shi ya sa nake murna cikin rashin ƙarfi, da zagi, da shan wahaloli, da tsanantawa, da matsaloli, saboda Kiristi. Don a sa’ad da nake marar ƙarfi a nan ne nake da ƙarfi.Gama ba da mutane da suke nama da jini ne muke yaƙi ba. Muna yaƙi ne da ikoki, da hukumomi, da masu mulkin duhu, da kuma a ikokin da suke cikin a sararin sama. Saboda haka sai ku yafa dukan kayan yaƙi na Allah, domin sa’ad da ranar mugun nan ta zo, ku iya yin tsayin daka, bayan kuma kuka gama kome, ku dāge.Tushe: OpenBible.info, CC BY 4.0 · Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi