Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Shahararrun ayoyin Littafi Mai Tsarki › Romawa 13:8

Ayar Littafi Mai Tsarki · SRK

Romawa 13:8

Kada hakkin kowa yă zauna a kanku, sai dai na ƙaunar juna, don mai ƙaunar maƙwabcinsa ya cika Doka ke nan.

Karanta dukan babin: Romawa 13

A cikin mahallinsa

5Saboda haka, dole a yi biyayya ga hukumomi, ba don gudun horo kawai ba amma don lamirinku.

6Shi ne ma ya sa kuke biyan haraji, gama hukumomin nan bayin Allah ne, waɗanda suke ba da dukan lokacinsu don aikin shugabanci.

7Ku ba wa kowa hakkinsa. In kuna da bashin haraji, sai ku biya; in kuɗin shiga ne, ku biya kuɗin shiga; in ladabi ne, ku yi ladabi; in kuma girmamawa ne, ku ba da girma.

8Kada hakkin kowa yă zauna a kanku, sai dai na ƙaunar juna, don mai ƙaunar maƙwabcinsa ya cika Doka ke nan.

9Umarnan nan, “Kada ka yi zina.” “Kada ka yi kisankai.” “Kada ka yi sata.” “Kada kuma ka yi ƙyashi.” Da dai duk sauran umarnai an ƙunshe su ne a wannan kalma “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.”

10Ƙauna ba ta cutar da maƙwabci. Saboda haka ƙauna cika Doka ce.

11Ku yi wannan domin kun san irin zamanin da kuke ciki. Lokaci ya yi da za ku farka daga barcinku, don cetonmu ya yi kusa yanzu fiye da lokacin da muka fara ba da gaskiya.

Romawa 13

Da Turanci

Berean Standard BibleRomans 13:8Be indebted to no one, except to one another in love. For he who loves his neighbor has fulfilled the law.

Nassoshi masu alaƙa

Sassan da masu karatu suka fi danganta wa da wannan.

Mat 22:39–40Ta biye kuma kamar ta farkon take. ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’ Dukan Doka da Annabawa suna rataya ne a kan waɗannan dokoki biyu.”
Gal 5:14Dukan doka an taƙaita a cikin umarni ɗaya ne cewa, “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.”
Mat 7:12Saboda haka, duk abin da kuke so mutane su yi muku, ku ma sai ku yi musu, domin wannan shi ne Doka da koyarwar Annabawa sun ƙunsa.
K Mag 3:27–28Kada ka ƙi yin alheri ga duk wanda ya dace, sa’ad da kana iya yin haka. Kada ka ce wa maƙwabcinka “Ka yă dakata sai gobe,” idan kana iya taimakonsa yanzu.
Yoh 13:34“Sabon umarni nake ba ku. Ku ƙaunaci juna. Kamar yadda na ƙaunace ku, ku ma ku ƙaunaci juna.
Yaƙ 2:8In fa kun kiyaye dokan nan ta mulki wadda take cikin Nassi mai cewa, “Ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka,” kun yi daidai.

Tushe: OpenBible.info, CC BY 4.0 · Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi