Bible Explorer Samu manhajar

Bincika › Hanyoyi › Dawuda ya gudu daga Absalom

Hanyoyi

Dawuda ya gudu daga Absalom

Ta Dutsen Zaitun zuwa Mahanayim, ya dawo ta Gilgal · tasha 7 · ≈ 130 km a layi madaidaici

UrushalimaBahurimMahanayimGilgal10 km123456

© OpenStreetMap contributors

Tashoshi

  1. Urushalima2Sam 15:14Sai Dawuda ya ce wa dukan fadawansa da suke tare da shi a Urushalima, “Ku zo! Mu gudu, in ba haka ba, babu wanda zai tsira daga hannun Absalom. Dole mu bar nan, nan da nan, in ba haka ba zai tashi da sauri yă fāɗa mana, yă kuma hallaka garin da takobi.”
  2. Kidron2Sam 15:23Dukan ƙauyuka suka yi ta kururuwa yayinda mutanen suke wucewa. Sarki shi ma ya haye ta Kwarin Kidron, mutane kuma suka ci gaba da tafiya zuwa wajen hamada.
  3. Dutsen Zaitun2Sam 15:30Amma Dawuda ya ci gaba yana hawan Dutsen Zaitun, yana kuka yayinda yake tafiya; kansa a rufe, kuma babu takalma a ƙafafunsa. Dukan mutanen da suke tare da shi suka rufe kawunansu suna ta kuka yayinda suke haurawa.
  4. Bahurim2Sam 16:5Yayinda Sarki Dawuda ya kusato Bahurim, sai ga wani mutumin dangin Shawulu ya fito daga can, sunansa Shimeyi ɗan Gera. Ya fito yana ta la’anta yayinda yake fitowa.
  5. Mahanayim2Sam 17:24Dawuda kuwa ya tafi Mahanayim. Absalom kuma ya ƙetare Urdun tare da dukan mutanen Isra’ila.
  6. Gilgal2Sam 19:15Sa’an nan sarki ya dawo, ya kuma tafi har zuwa Urdun. To, mutanen Yahuda suka zo Gilgal don su fita su taryi sarki, su kuma kawo shi ƙetaren Urdun.
  7. Urushalima2Sam 20:3Da Dawuda ya komo fadarsa a Urushalima, sai ya ɗauko ƙwarƙwaran goma nan da ya bari su lura da fada, ya keɓe su a wani gida inda za a yi tsaronsu. Ya tanada musu, amma bai kwana da su ba. Aka sa su a keɓe har iyakar rayuwarsu, suka yi zama kamar gwauraye.

Layukan suna haɗa tasoshi bisa jerin rubutun. Inda layi ke bin ƙasa, hanya ce mai yiwuwa kamar yadda wani masani ya sake gina ta; a wasu wurare madaidaici ne — ba a san hanyar ba. Nisan layi ne madaidaici tsakanin tasoshi. Ɗigo-ɗigo: ta jirgin ruwa. Masu haske: ba a tabbatar da wurin ba.

Kowane digo shi ne wurin da ya fi yiwuwa; digo mara haske yana nufin ba a tabbatar da wurin ba. Wuraren da ba a san inda suke ba ba sa kan taswira.

Tushe: OpenBible.info, CC BY 4.0 · UBS Bible Routes, Dr Leen Ritmeyer © United Bible Societies 2023, CC BY-SA 4.0 · Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi