Bible Explorer

Bincika › Hanyoyi › Tafiye-tafiyen Iliya

Hanyoyi

Tafiye-tafiyen Iliya

Daga Rafin Kerit zuwa Horeb da Urdun · tasha 13 · ≈ 1,210 km a layi madaidaici

12345678910111213

Tashoshi

  1. Gileyad1Sar 17:1To, Iliya mutumin Tishbe, daga Tishbe a Gileyad, ya ce wa Ahab, “Muddin Ubangiji, Allah na Isra’ila wanda nake bauta wa yana a raye, ba za a yi raɓa ko ruwan sama a ’yan shekaru masu zuwa ba, sai ko na faɗa haka.”
  2. Kerit1Sar 17:5Saboda haka sai Iliya ya yi abin da Ubangiji ya faɗa masa. Ya tafi Rafin Kerit, gabas da Urdun, ya zauna a can.
  3. Zarefat1Sar 17:10Saboda haka sai ya tafi Zarefat. Sa’ad da ya isa ƙofar gari, sai ga wata gwauruwa tana tattara ’yan itace. Sai ya kira ta, ya ce, “Ki kawo mini ɗan ruwa a tulu don in sha.”
  4. Dutsen Karmel1Sar 18:20Sai Ahab ya aika a duk fāɗin Isra’ila, ya kuma tattara annabawan a kan Dutsen Karmel.
  5. Kishon1Sar 18:40Sa’an nan Iliya ya umarce su, ya ce, “Ku kama annabawan Ba’al, kada ku bar waninsu yă tsere!” Suka kama su, Iliya kuwa ya sa aka gangara da su zuwa Kwarin Kishon, aka yayyanka su a can.
  6. Yezireyel1Sar 18:46Ikon Ubangiji ya sauko a kan Iliya, ya sha ɗamara, ya ruga a guje a gaban Ahab har zuwa Yezireyel.
  7. Beyersheba1Sar 19:3Iliya ya ji tsoro, ya gudu don yă ceci ransa. Sa’ad da ya kai Beyersheba a Yahuda, sai ya bar bawansa a can.
  8. Horeb1Sar 19:8Saboda haka ya tashi ya ci, ya kuma sha. Ta wurin ƙarfin da ya samu saboda wannan abinci, ya yi tafiya yini arba’in da dare arba’in, sai da ya kai Horeb, dutsen Allah.
  9. Damaskusba a faɗi isowa ba1Sar 19:15Sai Ubangiji ya ce masa, “Ka koma ta hanyar da ka zo, ka tafi Hamadan Damaskus. Sa’ad da ka kai can, ka shafe Hazayel yă zama sarki bisa Aram.
  10. Gilgal2Sar 2:1Da lokaci ya yi da Ubangiji zai ɗauki Iliya zuwa sama cikin guguwa, Iliya da Elisha kuwa suna kan hanyarsu daga Gilgal.
  11. Betel2Sar 2:2Sai Iliya ya ce wa Elisha, “Ka dakata a nan; Ubangiji ya aike ni Betel.” Amma Elisha ya amsa ya ce, “Muddin Ubangiji yana a raye, kai kuma kana a raye, ba zan rabu da kai ba.” Saboda haka suka gangara zuwa Betel.
  12. Yeriko2Sar 2:4Sai Iliya ya ce masa, “Ka dakata a nan Elisha; Ubangiji ya aike ni Yeriko.” Sai ya ce masa, “Muddin Ubangiji yana a raye, kai ma kana a raye, ba zan rabu da kai ba.” Saboda haka sai suka tafi Yeriko.
  13. Urdun2Sar 2:6Sai Iliya ya ce masa, “Ka dakata a nan, Ubangiji ya aike ni Urdun.” Sai Elisha ya ce masa, “Muddin Ubangiji yana a raye, kai kuma kana raye, ba zan rabu da kai ba.” Saboda haka suka ci gaba da tafiya tare.

Layukan suna haɗa tashoshin bisa ga jerin rubutun — ba a san hanyoyin kansu ba. Layin ɗigo-ɗigo: ta jirgin ruwa. Mara haske: ba a tabbatar da wurin ba.

Layin digo-digo: inda tafiyar take nufa — rubutun bai ce ta isa can ba; layin yana ci gaba daga tashar da ke gaba da ita.

Kowane digo shi ne wurin da ya fi yiwuwa (OpenBible.info); digo mara haske yana nufin ba a tabbatar da wurin ba. Wuraren da ba a san inda suke ba ba sa kan taswira.

Wurare: OpenBible.info Bible Geocoding Data (CC BY 4.0).

Iyakokin ƙasa: Natural Earth (mallakar jama’a).