Bible Explorer

Bincika › Hanyoyi › Dawuda yana gudu

Hanyoyi

Dawuda yana gudu

Yana gudu daga Shawulu, sa’an nan sarki a Hebron da Urushalima · tasha 13 · ≈ 420 km a layi madaidaici

12345678910111213

Tashoshi

  1. Rama1Sam 19:18Da Dawuda ya gudu ya tsere, sai ya tafi wurin Sama’ila a Rama ya gaya masa dukan abin da Shawulu ya yi masa. Da shi da Sama’ila suka tafi Nayiwot suka zauna a can.
  2. Nob1Sam 21:1Dawuda ya tafi Nob a wurin Ahimelek firist. Da Ahimelek ya gan shi sai ya firgita ya ce, “Me ya sa kai kaɗai ne? Me ya sa ba wani tare da kai?”
  3. Gat1Sam 21:10A ranar, Dawuda ya gudu daga wajen Shawulu ya tafi wuri Akish sarkin Gat.
  4. Adullam1Sam 22:1Dawuda ya bar Gat, ya tsere zuwa kogon Adullam. Da ’yan’uwansa da kuma iyalan mahaifinsa suka ji labari, sai suka tafi can wurinsa.
  5. Mizfa1Sam 22:3Daga can Dawuda ya tafi Mizfa a Mowab. Ya ce wa sarkin Mowab, “Za ka yarda mahaifina da mahaifiyata su zo su zauna a wurinka kafin in san abin da Allah zai yi da ni?”
  6. Heret1Sam 22:5Amma annabin nan Gad ya ce wa Dawuda, “Kada ka zauna a nan, maza ka tashi ka shiga ƙasar Yahuda”. Sai Dawuda ya tashi ya tafi jejin Heret.
  7. Keyila1Sam 23:5Sa’an nan Dawuda da mutanensa suka tafi Keyila, suka yi yaƙi da Filistiyawa, suka kwashe musu shanunsu, suka jijji wa Filistiyawa ƙwarai, suka cece mutanen Keyila daga hannunsu.
  8. Zif1Sam 23:14Dawuda ya zauna a jeji cikin kogunan duwatsu da kuma tuddan jejin Zif. Kowace rana Shawulu ya yi ta neman Dawuda amma Allah bai bashe Dawuda a hannunsa ba.
  9. Mawon1Sam 23:24Sai suka tashi suka koma Zif, suka sha gaban Shawulu. Dawuda da mutanensa kuwa suna jejin Mawon cikin Araba, kudu da Yeshimon.
  10. En Gedi1Sam 23:29Dawuda kuwa ya haura daga can ya zauna a kogwannin duwatsun En Gedi.
  11. Ziklag1Sam 27:6A ranar Akish ya ba shi Ziklag wanda tun dā take ta sarkin Yahuda.
  12. Hebron2Sam 2:1Bayan ’yan kwanaki, sai Dawuda ya nemi nufin Ubangiji ya ce, “In haura zuwa ɗaya daga cikin biranen Yahuda?” Ubangiji ya ce, “Haura.” Dawuda ya ce, “Wanne zan tafi?” Ubangiji ya ce, “Je Hebron.”
  13. Urushalima2Sam 5:6Sarki da mutanensa suka tafi Urushalima don su kai wa Yebusiyawan da suke zaune a can hari, Yebusiyawa suka ce wa Dawuda, “Ba za ka shiga nan ba; ko makafi da guragu kaɗai ma za su kore ka.” Suka yi tsammani suna cewa, “Dawuda ba zai iya shiga can ba.”

Layukan suna haɗa tashoshin bisa ga jerin rubutun — ba a san hanyoyin kansu ba. Layin ɗigo-ɗigo: ta jirgin ruwa. Mara haske: ba a tabbatar da wurin ba.

Kowane digo shi ne wurin da ya fi yiwuwa (OpenBible.info); digo mara haske yana nufin ba a tabbatar da wurin ba. Wuraren da ba a san inda suke ba ba sa kan taswira.

Wurare: OpenBible.info Bible Geocoding Data (CC BY 4.0).

Iyakokin ƙasa: Natural Earth (mallakar jama’a).