Bincika › Littattafan Bishara gefe da gefe › Koyarwa
Littattafan Bishara gefe da gefe · Koyarwa
Addu’ar Ubangiji
Mat 6:9–13 · Luk 11:2–4
Mat 6:9–139“To, ga yadda ya kamata ku yi addu’a. “ ‘Ubanmu wanda yake cikin sama, a tsarkake sunanka,
10mulkinka yă zo a aikata nufinka a duniya kamar yadda ake yi a sama.
11Ka ba mu yau abincin yininmu.
12Ka gafarta mana laifofinmu, kamar yadda mu ma muke gafarta wa masu yin mana laifi.
13Kada ka bari a kai mu cikin jarraba, amma ka cece mu daga mugun nan. ’
Luk 11:2–42Sai ya ce musu, “Sa’ad da kuke yin addu’a ku ce, “ ‘Ya Uba, sunanka mai tsarki ne mulkinka ya zo.
3Ka ba mu kowace rana abincin yini.
4Ka gafarta mana zunubanmu, kamar yadda mu ma ke gafarta wa duk wanda ya yi mana laifi. Kada ka bari a kai mu cikin jarraba.’ ”
An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY