Bible Explorer

Gida › Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce › Kalamai da magana

Dangantaka

Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da Kalamai da magana

Ayoyin da masu karatu suka fi komawa gare su don wannan jigo (15), an ambace su gaba ɗaya daga Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa.

Afi 4:29Kada wata ƙazamar magana ta fita daga bakunanku, sai dai abin da yake da amfani don gina waɗansu bisa ga bukatunsu. Ta haka maganarku za tă zama da amfani ga masu jinta.
K Mag 18:21Harshe yana da ikon rai da mutuwa, kuma waɗanda suke ƙaunarsa za su ci amfaninsa.
Yaƙ 1:26In wani ya ɗauki kansa mai addini ne duk da haka bai ƙame harshensa ba, ruɗin kansa yake yi addininsa kuwa banza ne.
K Mag 15:1Amsa da tattausar harshe kan kwantar da fushi, amma magana da kakkausan harshe kan kuta fushi.
K Mag 21:23Duk wanda yake lura da bakinsa da kuma harshensa kan kiyaye kansa daga masifa.
K Mag 12:18Maganganun rashin tunani sukan soki mutum kamar takobi, amma harshen mai hikima kan kawo warkarwa.
K Mag 15:4Harshen da ya kawo warkarwa shi ne itacen rai, amma harshe mai ƙarya kan ragargaza zuciya.
1Bit 3:10Gama, “Duk wanda yake so yă ji daɗin rayuwa, yă kuma ga kwanaki masu kyau dole yă ƙame harshensa daga mugunta leɓunansa kuma daga maganar yaudara.
Zab 141:3Ka sa mai tsaro a bakina, ya Ubangiji; ka yi tsaron ƙofar leɓunana.
K Mag 10:19Sa’ad da magana ta yi yawa, ba a rasa zunubi a ciki, amma shi da ya ƙame harshensa mai hikima ne.
Yaƙ 3:8amma ba mutumin da zai iya ya sarrafa harshe. Mugu ne marar hutu, cike da dafi mai kisa.
Zab 19:14Bari kalmomin bakina da tunanin zuciyata su zama abin gamsuwa a gabanka, Ya Ubangiji, Dutsena da Mai fansata.
Zab 34:13ka kiyaye harshenka daga mugunta da kuma leɓunanku daga faɗar ƙarairayi.
Mat 15:11Abin da yake shiga bakin mutum ba ya ƙazantar da shi, sai dai abin da yake fitowa daga bakinsa, shi ne yake ƙazantar da shi.”
K Mag 16:24Kalmomi masu daɗi suna kama da kakin zuma, mai zaƙi ga rai da kuma warkarwa ga ƙasusuwa.

Waɗannan ayoyi ne da masu karatu suka fi komawa a wannan batu — ba koyarwa a kansa ba. Karanta kowanne a cikin surarsa.

Tushe

Ayoyin kowane jigo da tsarinsu: bayanan jigogi na OpenBible.info, bisa ƙuri’un masu karatu: OpenBible.info · CC BY 4.0

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.