Bible Explorer

Gida › Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce › Gulma

Dangantaka

Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da Gulma

Ayoyin da masu karatu suka fi komawa gare su don wannan jigo (12), an ambace su gaba ɗaya daga Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa.

K Mag 16:28Fitinannen mutum yakan zuga tashin hankali, mai gulma kuma yakan raba abokai na kusa.
K Mag 26:20In ba itace wuta takan mutu; haka kuma in ba mai gulma ba za a yi faɗa ba.
K Mag 20:19Mai gulma yakan lalace yarda; saboda haka ka guji mutum mai yawan surutu.
1Tim 5:13Ban da haka, sukan koyi zaman banza, suna zirga-zirga gida-gida. Ba kawai sun zama masu zaman banza ba, har ma sun zama masu gulma da masu shisshigi, suna faɗin abubuwan da bai kamata su faɗa ba.
K Mag 11:13Gulma yakan lalace yarda, amma mutum mai aminci kan kiyaye asiri.
Fir 19:16“ ‘Kada ku yi ta yawo kuna yaɗa ƙarya a cikin mutanenku. “ ‘Kada ku yi wani abin da zai sa ran maƙwabcinku cikin hatsari. Ni ne Ubangiji.
K Mag 18:8Kalmomin mai gulma kamar abinci mai daɗi suke; sukan gangara zuwa can cikin gaɓoɓin mutum.
K Mag 10:18Duk wanda ya ɓoye ƙiyayyarsa yana da ƙarya a leɓunansa, duk kuma wanda yake baza ƙarairayi wawa ne.
Fit 23:1“Kada ku baza rahoton ƙarya. Kada kuma ku haɗa baki da mugayen mutane har da ku zama munafukai ta wurin ba da shaidar ƙarya.
Yaƙ 4:11’Yan’uwa, kada ku ɓata wa juna suna. Duk wanda ya zargi ɗan’uwansa ko ya ɗora masa laifi, yana gāba da doka ne yana kuma yin mata shari’a ke nan. In kuwa ka ɗora wa shari’a laifi, kai ba mai binta ba ne, mai ɗora mata laifi ne.
Zab 101:5Duk wanda ya yi ɓatanci wa maƙwabcinsa a ɓoye shi za a kashe; duk mai renin wayo da mai girman kai, ba zan jure masa ba.
Mat 12:36Amma ina gaya muku cewa mutane za su ba da lissafi a ranar shari’a a kan kowace kalmar banza da suka faɗa.

Waɗannan ayoyi ne da masu karatu suka fi komawa a wannan batu — ba koyarwa a kansa ba. Karanta kowanne a cikin surarsa.

Tushe

Ayoyin kowane jigo da tsarinsu: bayanan jigogi na OpenBible.info, bisa ƙuri’un masu karatu: OpenBible.info · CC BY 4.0

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.