Bible Explorer

Gida › Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce › Ƙaunar maƙwabcinka

Dangantaka

Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da Ƙaunar maƙwabcinka

Ayoyin da masu karatu suka fi komawa gare su don wannan jigo (14), an ambace su gaba ɗaya daga Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa.

Fir 19:18“ ‘Kada ka nemi yin ramuwa, ko ka riƙe wani cikin mutanenka a zuciya, amma ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka. Ni ne Ubangiji.
Mar 12:31Na biyun ita ce, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’ Ba wata doka da ta fi waɗannan.”
Mat 22:39Ta biye kuma kamar ta farkon take. ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’
Yaƙ 2:8In fa kun kiyaye dokan nan ta mulki wadda take cikin Nassi mai cewa, “Ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka,” kun yi daidai.
Rom 13:8–10Kada hakkin kowa yă zauna a kanku, sai dai na ƙaunar juna, don mai ƙaunar maƙwabcinsa ya cika Doka ke nan. Umarnan nan, “Kada ka yi zina.” “Kada ka yi kisankai.” “Kada ka yi sata.” “Kada kuma ka yi ƙyashi.” Da dai duk sauran umarnai an ƙunshe su ne a wannan kalma “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.” Ƙauna ba ta cutar da maƙwabci. Saboda haka ƙauna cika Doka ce.
Gal 5:14Dukan doka an taƙaita a cikin umarni ɗaya ne cewa, “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.”
Gal 6:2Ku ɗauki nawayar juna, a haka kuwa za ku cika dokar Kiristi.
Mat 7:12Saboda haka, duk abin da kuke so mutane su yi muku, ku ma sai ku yi musu, domin wannan shi ne Doka da koyarwar Annabawa sun ƙunsa.
Fil 2:4Bai kamata kowannenku yă kula da sha’anin kansa kawai ba, sai dai yă kula da sha’anin waɗansu ma.
Ibr 13:16Kada kuma ku manta yin aikin nagari da kuma taimakon waɗansu, gama da irin waɗannan hadayu ne Allah yake jin daɗi.
1Yoh 3:17–18In wani yana da arziki, ya kuma ga ɗan’uwansa cikin rashi, bai kuwa taimake shi ba, anya, ƙaunar Allah tana a cikinsa kuwa? ’Ya’yana ƙaunatattu, kada mu yi ƙauna da fatar baki kawai, sai dai mu nuna ta ta wurin aikatawa da kuma gaskiya.
1Bit 4:9Ku riƙa karɓar juna ba da gunaguni ba.
1Tes 5:14Muna kuma gargaɗe ku, ’yan’uwa, ku gargaɗe waɗanda suke zaman banza, ku ƙarfafa masu raunanar zuciya, ku taimaki marasa ƙarfi, ku yi haƙuri da kowa.
K Mag 14:21Duk wanda ya rena maƙwabci ya yi zunubi, amma mai albarka ne wanda yake alheri ga mabukata.

Waɗannan ayoyi ne da masu karatu suka fi komawa a wannan batu — ba koyarwa a kansa ba. Karanta kowanne a cikin surarsa.

Tushe

Ayoyin kowane jigo da tsarinsu: bayanan jigogi na OpenBible.info, bisa ƙuri’un masu karatu: OpenBible.info · CC BY 4.0

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.