Bible Explorer

Gida › Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce › Abota

Dangantaka

Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da Abota

Ayoyin da masu karatu suka fi komawa gare su don wannan jigo (15), an ambace su gaba ɗaya daga Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa.

K Mag 18:24Mutum mai abokai masu yawa kan lalace, amma akwai abokin da yakan manne kurkusa fiye da ɗan’uwa.
K Mag 17:17Aboki yakan yi ƙauna a koyaushe, ɗan’uwa kuma, ai, don ɗaukar nawayar juna ne aka haife shi.
K Mag 27:17Kamar yadda ƙarfe kan wasa ƙarfe haka mutum kan koyi daga mutum.
Yoh 15:13Babu ƙaunar da ta fi wannan, a ce mutum ya ba da ransa saboda abokansa.
K Mag 27:9Man shafawa mai ƙanshi da kuma turare kan faranta zuciya, gaisuwar amini kuma takan fito daga shawarar kirki.
1Kor 15:33Kada fa a ruɗe ku, “Ajiyar mugayen abokai yana ɓata hali mai kyau.”
K Mag 16:28Fitinannen mutum yakan zuga tashin hankali, mai gulma kuma yakan raba abokai na kusa.
K Mag 27:6Za a iya amince da rauni daga aboki, amma abokin gāba ko da ya sumbace ka kada ka sake da shi!
K Mag 22:24–25Kada ka yi abokantaka da mai zafin rai, kada ka haɗa kai da wanda ba shi da wuya ya yi fushi, in ba haka ba za ka koyi hanyoyinsa ka kuma sa kanka a tarko.
K Mag 13:20Shi da yake tafiya tare da masu hikima yakan ƙaru da hikima, amma abokin wawaye zai yi fama da lahani.
K Mag 12:26Adali yakan yi hankali a abokantaka, amma hanyar mugaye kan kai su ga kaucewa.
M Had 4:9–10Biyu sun fi ɗaya, gama suna samun riba mai kyau na aikinsu. In ɗaya ya fāɗi, abokinsa zai taimake shi yă tashi. Amma abin tausayi ne ga mutumin da ya fāɗi ba shi kuma da wanda zai taimake shi yă tashi!
K Mag 17:9Duk wanda ya rufe laifi yana inganta ƙauna ne, amma duk wanda ya yi ta maimaita batu yakan raba abokai na kusa.
Ayu 6:14“Duk wanda ya ƙi yă yi alheri ga aboki ya rabu ta tsoron Maɗaukaki.
1Bit 4:8–10Fiye da kome, ku ƙaunaci juna sosai, domin ƙauna tana rufe zunubai masu ɗumbun yawa. Ku riƙa karɓar juna ba da gunaguni ba. Kowa yă yi amfani da kowace baiwar da ya samu don kyautata wa waɗansu, cikin aminci yana aikata alherin Allah a hanyoyi dabam-dabam.

Waɗannan ayoyi ne da masu karatu suka fi komawa a wannan batu — ba koyarwa a kansa ba. Karanta kowanne a cikin surarsa.

Tushe

Ayoyin kowane jigo da tsarinsu: bayanan jigogi na OpenBible.info, bisa ƙuri’un masu karatu: OpenBible.info · CC BY 4.0

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.