Bible Explorer

Gida › Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce › Rikici da sulhu

Dangantaka

Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da Rikici da sulhu

Ayoyin da masu karatu suka fi komawa gare su don wannan jigo (10), an ambace su gaba ɗaya daga Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa.

Mat 5:9Masu albarka ne waɗanda suke masu ƙulla zumunci, gama za a kira su ’ya’yan Allah.
K Mag 15:1Amsa da tattausar harshe kan kwantar da fushi, amma magana da kakkausan harshe kan kuta fushi.
Zab 34:14Juyo daga mugunta ku yi alheri; nemi salama ku kuma yi ƙoƙarin samunta.
Yaƙ 4:1–2Me yake jawo faɗace-faɗace da gardandami a tsakaninku? Ashe, ba sha’awace-sha’awacenku da suke yaƙi a zukatanku ba ne? Kukan nemi abu ku rasa, sai ku yi kisa da ƙyashi. In kuka rasa abin da kuke nema sai ku shiga yin gardama da faɗa. Kukan rasa ne, domin ba ku roƙi Allah ba.
Mat 18:15–17“In ɗan’uwanka ya yi maka laifi, ka je ka nuna masa laifinsa, tsakaninku biyu kaɗai. In ya saurare ka, ka maido da ɗan’uwanka ke nan. Amma in bai saurare ka ba, ka je tare da mutum ɗaya ko biyu, domin ‘a tabbatar da kowace magana a bakin shaidu biyu ko uku.’ In kuwa ya ƙi yă saurare su, sai ka gaya wa ikkilisiya; in kuma ya ƙi yă saurari ikkilisiya ma, ka yi da shi kamar marar sanin Allah ko mai karɓar haraji.
Afi 4:26“Cikin fushinku kada ku yi zunubi.” Kada ku bar rana ta fāɗi kuna fushi,
Rom 14:19Saboda haka sai mu yi iya ƙoƙari mu aikata abin da zai kawo salama da kuma ingantawa ga juna.
2Tim 2:23–24Kada wani abu yă haɗa ka da gardandamin banza da wofi, domin ka san yadda suke jawo faɗa. Bai kamata bawan Ubangiji yă zama mai neman faɗa ba; a maimako, dole yă nuna alheri ga kowa, mai iya koyarwa, mai haƙuri kuma.
Rom 12:18Ku yi iya ƙoƙarinku, in zai yiwu, ku yi zaman lafiya da kowa.
Yaƙ 1:19’Yan’uwana ƙaunatattu, ku lura da wannan. Ya kamata kowa yă kasance mai saurin saurara, ba mai saurin magana ba, ba kuma mai saurin fushi ba,

Waɗannan ayoyi ne da masu karatu suka fi komawa a wannan batu — ba koyarwa a kansa ba. Karanta kowanne a cikin surarsa.

Tushe

Ayoyin kowane jigo da tsarinsu: bayanan jigogi na OpenBible.info, bisa ƙuri’un masu karatu: OpenBible.info · CC BY 4.0

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.