Gida › Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce › Cin amana da raunin zuciya
Dangantaka
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da Cin amana da raunin zuciya
Ayoyin da masu karatu suka fi komawa gare su don wannan jigo (10), an ambace su gaba ɗaya daga Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa.
Mik 7:5–6
Kada ka yarda da maƙwabci; kada ka sa begenka ga abokai. Ko ma wadda take kwance a ƙirjinka, ka yi hankali da kalmominka. Gama ɗa yakan ce wannan ba mahaifinsa ba ne, diya kuma takan tayar wa mahaifiyarta, matar ɗa takan yi gāba da uwar mijinta, abokan gāban mutum su ne iyalin cikin gidansa.Mar 11:25
A duk lokacin da kuke tsaye cikin addu’a, in kuna riƙe da wani mutum a zuciyarku, ku gafarta masa, domin Ubanku da yake sama shi ma yă gafarta muku zunubanku.”Zab 118:8
Ya fi kyau in nemi mafaka a wurin Ubangiji da in dogara ga mutum.Mat 6:14–15
Gama in kuna yafe wa mutane sa’ad da suka yi muku laifi, Ubanku da yake cikin sama ma zai gafarta muku. Amma in ba kwa yafe wa mutane laifofinsu, Ubanku ma ba zai gafarta muku zunubanku ba.Zab 34:18
Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai ya kuma cece waɗanda aka ragargaza a ruhu.Luk 6:27
“Amma ina faɗa muku, ku da kuke ji na, ku ƙaunaci abokan gābanku, ku yi wa masu ƙinku alheri.Zab 41:9
Har abokina na kurkusa, wanda na amince da shi, wanda muke cin abinci tare, ya juya yana gāba da ni.Luk 21:16
Har iyayenku, da ’yan’uwanku maza, da danginku, da abokanku ma, duk za su bashe ku, su kuma kashe waɗansunku.Luk 22:48
Amma Yesu ya tambaye shi ya ce, “Yahuda, ashe, da sumba za ka bashe Ɗan Mutum?”Rom 12:19
Kada ku yi ramuwa, abokaina, sai dai ku bar wa Allah. Gama a rubuce yake cewa, “Ramuwa tawa ce; zan kuwa sāka,” in ji Ubangiji.Waɗannan ayoyi ne da masu karatu suka fi komawa a wannan batu — ba koyarwa a kansa ba. Karanta kowanne a cikin surarsa.
Tushe
Ayoyin kowane jigo da tsarinsu: bayanan jigogi na OpenBible.info, bisa ƙuri’un masu karatu: OpenBible.info · CC BY 4.0
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.