Bible Explorer

Gida › Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce › Karɓar baƙi

Dangantaka

Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da Karɓar baƙi

Ayoyin da masu karatu suka fi komawa gare su don wannan jigo (10), an ambace su gaba ɗaya daga Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa.

Ibr 13:2Kada ku manta da yin alheri ga baƙi, gama ta yin haka ne waɗansu suka yi wa mala’iku hidima, ba da saninsu ba.
1Bit 4:9Ku riƙa karɓar juna ba da gunaguni ba.
Rom 12:13Ku taimaki mutanen Allah masu bukata. Ku zama masu karɓan baƙi.
Fir 19:34Dole ku ɗauki baƙon da yake zama tare da ku kamar haifaffe ɗan ƙasa. Ku ƙaunace shi kamar kanku, gama dā ku ma baƙi ne a Masar. Ni ne Ubangiji Allahnku.
Luk 14:12–14Sai Yesu ya ce wa wanda ya gayyace shi, “Lokacin da ka shirya biki ko liyafa, kada ka gayyaci abokanka, ko ’yan’uwanka, ko danginka, ko kuma maƙwabtanka masu arziki, gama in ka yi haka, suna iya gayyatarka, su biya maka alherin da ka yi musu. Amma lokacin da ka kira biki, ka gayyaci matalauta, da guragu, da shanyayyu, da makafi. Ta haka, za ka sami albarka. Ko da yake ba za su iya biyan ka ba, za a biya ka a ranar tashin masu adalci daga matattu.”
Ayy M 28:2Mutanen tsibirin kuwa suka nuna mana babban alheri. Suka hura wuta suka marabce mu duka saboda ana ruwan sama da kuma sanyi.
Mar 9:41Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ya ba ku ruwan sha a sunana, saboda ku na Kiristi ne, lalle, ba zai rasa ladarsa ba.
Mat 25:35Gama da nake jin yunwa, kun ciyar da ni, da nake jin ƙishirwa, kun ba ni abin sha, da nake baƙunci, kun karɓe ni,
M Sh 10:19Sai ku ƙaunaci baƙi, gama dā ku ma baƙi ne a ƙasar Masar.
Mat 25:40“Sarkin zai amsa ya ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, duk abin da kuka yi wa ɗaya daga cikin waɗannan ’yan’uwana mafi ƙanƙanta, ni kuka yi wa.’

Waɗannan ayoyi ne da masu karatu suka fi komawa a wannan batu — ba koyarwa a kansa ba. Karanta kowanne a cikin surarsa.

Tushe

Ayoyin kowane jigo da tsarinsu: bayanan jigogi na OpenBible.info, bisa ƙuri’un masu karatu: OpenBible.info · CC BY 4.0

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.