Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Shahararrun ayoyin Littafi Mai Tsarki › Yohanna 15:13

Ayar Littafi Mai Tsarki · SRK

Yohanna 15:13

Babu ƙaunar da ta fi wannan, a ce mutum ya ba da ransa saboda abokansa.

Karanta dukan babin: Yohanna 15

A cikin mahallinsa

10In kuka yi biyayya da umarnaina, za ku kasance a cikin ƙaunata, kamar dai yadda na yi biyayya da umarnan Ubana na kuma kasance a cikin ƙaunarsa.

11Na gaya muku wannan domin murnata ta kasance a cikinku, murnanku kuma ta zama cikakkiya.

12Umarnina shi ne, Ku ƙaunaci juna kamar yadda na ƙaunace ku.

13Babu ƙaunar da ta fi wannan, a ce mutum ya ba da ransa saboda abokansa.

14Ku abokaina ne, in kun yi abin da na umarta.

15Ba zan ƙara ce da ku bayi ba, don bawa bai san abin da maigidansa yake yi ba. A maimako in ce da ku abokai, domin na sanar da ku duk abin da na ji daga wurin Ubana.

16Ba ku kuka zaɓe ni ba, a’a, ni ne na zaɓe ku na kuma naɗa ku ku je ku ba da ’ya’ya-’ya’yan da za su dawwama. Uba kuwa zai ba ku duk abin da kuka roƙa cikin sunana.

Yohanna 15

Da Turanci

Berean Standard BibleJohn 15:13Greater love has no one than this, that he lay down his life for his friends.

Nassoshi masu alaƙa

Sassan da masu karatu suka fi danganta wa da wannan.

Yoh 10:11“Ni ne makiyayi mai kyau. Makiyayi mai kyau yakan ba da ransa domin tumakin.
Afi 5:2ku kuma yi rayuwar ƙauna, kamar yadda Kiristi ya ƙaunace mu, har ya ba da kansa dominmu a matsayin sadaka mai ƙanshi da kuma hadaya ga Allah.
Rom 5:6–8Kun ga, a daidai lokaci, yayinda muke marasa ƙarfi, Kiristi ya mutu saboda waɗanda ba su san Allah ba. Da ƙyar wani yă mutu saboda mai adalci, ko da yake saboda mutumin kirki wani zai iya ƙarfin hali yă mutu. Amma Allah ya nuna mana ƙaunarsa a wannan. Tun muna masu zunubi tukuna, Kiristi ya mutu dominmu.
Yoh 10:15kamar yadda Uba ya san ni, ni kuma na san Uba, ina kuwa ba da raina domin tumakin.
1Yoh 4:7–11Abokaina ƙaunatattu, mu ƙaunaci juna, domin ƙauna tana zuwa daga Allah ne. Duk mai ƙauna, haifaffe ne na Allah, ya kuma san Allah. Duk wanda ba ya ƙauna, bai san Allah ba, domin Allah ƙauna ne. Ga yadda Allah ya nuna ƙaunarsa a cikinmu, Allah ya aiki makaɗaici Ɗansa zuwa duniya domin mu rayu ta wurinsa. Wannan ita ce ƙauna, wato, ba mu ne muka ƙaunaci Allah ba, sai dai shi ne ya ƙaunace mu, ya kuma aiko Ɗansa yă zama hadaya ta kafara saboda zunubanmu. Abokaina ƙaunatattu, da yake Allah ya ƙaunace mu haka, ya kamata mu ma mu ƙaunaci juna.

Tushe: OpenBible.info, CC BY 4.0 · Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi