Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Shahararrun ayoyin Littafi Mai Tsarki › Galatiyawa 6:9

Ayar Littafi Mai Tsarki · SRK

Galatiyawa 6:9

Kada mu gaji da yin nagarta, gama a daidai lokaci za mu girbe amfani, in ba mu fid da zuciya ba.

Karanta dukan babin: Galatiyawa 6

A cikin mahallinsa

6Duk haka, wanda aka koya wa maganar Kiristi, bari yă raba abubuwan nan na alheri tare da wanda ya koyar da shi.

7Kada a ruɗe ku. Ba a yi wa Allah ba’a. Mutum yakan girbe abin da ya shuka ne.

8Wanda ya yi shuki don yă gamshi mutuntakarsa, daga wannan mutuntaka zai girbi hallaka. Wanda ya yi shuki domin yă gamshi Ruhu, daga Ruhu zai girbi rai madawwami.

9Kada mu gaji da yin nagarta, gama a daidai lokaci za mu girbe amfani, in ba mu fid da zuciya ba.

10Saboda haka, in da hali, bari mu aikata nagarta ga dukan mutane, musamman ga waɗanda suke na iyalin masu bi.

11Ku dubi irin manya-manyan harufan da na yi amfani da su yayinda nake rubuta muku da hannuna!

12Waɗanda suke son nuna bajinta a fili suna ƙoƙari su tilasta muku ku yi kaciya ne. Dalilin kaɗai da suke yin haka shi ne don gudu kada a tsananta musu saboda gicciyen Kiristi ne.

Galatiyawa 6

Da Turanci

Berean Standard BibleGalatians 6:9Let us not grow weary in well-doing, for in due time we will reap a harvest if we do not give up.

Nassoshi masu alaƙa

Sassan da masu karatu suka fi danganta wa da wannan.

1Kor 15:58Saboda haka, ƙaunatattu ’yan’uwana, ku tsaya da daram. Kada wani abu yă jijjiga ku. Ku ba da kanku kullum ga aikin Ubangiji, domin kun san cewa famar da kuke yi saboda Ubangiji ba a banza take ba.
2Tes 3:13Game da ku kuma ’yan’uwa, kada ku gaji da yin abin da yake daidai.
Ish 40:30–31Ko matasa ma kan gaji su kuma kasala, samari kuma kan yi tuntuɓe su fāɗi; amma waɗanda suka dogara ga Ubangiji za su sabunta ƙarfinsu. Za su yi firiya da fikafikai kamar gaggafa; za su kuma yi gudu ba kuwa za su gaji ba, za su yi tafiya ba kuwa za su kasala ba.
Ibr 10:35–39Saboda haka kada ku yar da tabbacinku; za a sāka muku a yalwace. Kuna bukata ku jimre don sa’ad da kuka aikata nufin Allah, za ku karɓi abin da ya yi alkawari. Gama, “A cikin ɗan lokaci kaɗan, mai zuwan nan zai zo ba kuwa zai yi jinkiri ba. Amma, “Mai adalcina zai rayu ta wurin bangaskiya. In kuwa ya ja da baya, ba zan ji daɗinsa ba.” Amma mu ba na waɗanda suke ja da baya, su kuma hallaka ba ne, amma na waɗanda suka gaskata, suka kuma sami ceto ne.
Ibr 12:3Ku lura da wannan wanda ya jure da irin hamayyan nan daga masu zunubi, don kada ku gaji, har ku fid da zuciya.
1Bit 2:15Gama nufin Allah ne cewa ta wurin yin nagarta za ku toshe jahilcin marasa azanci.
Yaƙ 5:7Saboda haka ’yan’uwa, sai ku yi haƙuri har dawowar Ubangiji. Ku dubi yadda manomi yakan jira gona ta ba da amfaninta mai kyau, da kuma yadda yake haƙurin jiran ruwan sama na damina da na kaka.
1Bit 3:17Ya fi kyau, in nufin Allah ne, a sha wahala don yin nagarta fiye da yin mugunta.

Tushe: OpenBible.info, CC BY 4.0 · Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi