Gida › Shahararrun ayoyin Littafi Mai Tsarki › Karin Magana 22:7
Ayar Littafi Mai Tsarki · SRK
Karin Magana 22:7
Mawadaci yakan yi mulki a kan matalauci, mai cin bashi kuwa bawan mai ba da bashi ne.
Karanta dukan babin: Karin Magana 22
A cikin mahallinsa
4Sauƙinkai da tsoron Ubangiji sukan kawo wadata da girmamawa da kuma rai.
5A hanyoyin mugu akwai kaya da tarko, amma duk wanda ya kiyaye ransa kan kauce musu.
6Ka hori yaro a hanyar da ya kamata yă bi, kuma sa’ad da ya tsufa ba zai bar ta ba.
7Mawadaci yakan yi mulki a kan matalauci, mai cin bashi kuwa bawan mai ba da bashi ne.
8Duk wanda ya shuka mugunta yakan girbe wahala, za a kuma hallaka sandar fushinsa.
9Mai bayarwa hannu sake shi kansa zai sami albarka, gama yakan raba abincinsa da matalauta.
10Ka hori mai ba’a, hatsaniya kuwa za tă yi waje; fitina da zargi kuma za su ƙare.
Da Turanci
The rich rule over the poor, and the borrower is slave to the lender.Nassoshi masu alaƙa
Sassan da masu karatu suka fi danganta wa da wannan.
Matar wani daga ƙungiyar annabawa ta yi wa Elisha kuka ta ce, “Mijina, bawanka, ya mutu, ka kuma san yadda ya girmama Ubangiji. Amma ga shi yanzu mai binsa bashi ya zo yă kwashe ’ya’yana maza biyu su zama bayinsa.”Tushe: OpenBible.info, CC BY 4.0 · Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi