Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Shahararrun ayoyin Littafi Mai Tsarki › 1 Tessalonikawa 4:3–5

Ayar Littafi Mai Tsarki · SRK

1 Tessalonikawa 4:3–5

3Nufin Allah ne a tsarkake ku, cewa ku guje wa fasikanci;

4don kowannenku yă koya yadda zai ƙame kansa a hanyar da take mai tsarki, mai mutunci kuma,

5ba cikin muguwar sha’awa kamar ta marasa bangaskiya, waɗanda ba su san Allah ba;

Karanta dukan babin: 1 Tessalonikawa 4

A cikin mahallinsa

1A ƙarshe, ’yan’uwa, mun umarce ku yadda za ku yi rayuwa domin ku gamshi Allah, kamar yadda kuke yi. Yanzu muna roƙonku muna kuma gargaɗe ku a cikin Ubangiji Yesu ku yi haka sau da sau.

2Gama kun san umarnan da muka ba ku ta wurin ikon Ubangiji Yesu.

3Nufin Allah ne a tsarkake ku, cewa ku guje wa fasikanci;

4don kowannenku yă koya yadda zai ƙame kansa a hanyar da take mai tsarki, mai mutunci kuma,

5ba cikin muguwar sha’awa kamar ta marasa bangaskiya, waɗanda ba su san Allah ba;

6cikin wannan al’amari kuwa kada wani yă yi wa ɗan’uwansa laifi ko yă cuce shi. Ubangiji zai hukunta mutane saboda dukan irin waɗannan zunubai, kamar yadda muka riga muka gaya muku, muka kuma yi muku gargaɗi.

7Gama Allah bai kira mu ga zaman marasa tsarki ba, sai dai ga zaman tsarki.

8Saboda haka, duk wanda ya ƙi wannan umarni ba mutum ne ya ƙi ba sai ko Allah, wanda ya ba ku Ruhunsa Mai Tsarki.

1 Tessalonikawa 4

Da Turanci

Berean Standard Bible1 Thessalonians 4:3–5For it is God’s will that you should be holy: You must abstain from sexual immorality; each of you must know how to control his own body in holiness and honor, not in lustful passion like the Gentiles who do not know God;

Nassoshi masu alaƙa

Sassan da masu karatu suka fi danganta wa da wannan.

1Bit 4:2Ta haka, ba ya sauran rayuwarsa a kan mugayen sha’awace-sha’awacen jiki, sai dai nufin Allah.
Rom 12:2Kada ku ci gaba da yin abin da duniya take yi, sai dai ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so yake, abu mai kyau, mai daɗi da kuma cikakke.
1Tes 5:23Bari Allah da kansa, Allah na salama, yă tsarkake ku sarai. Bari dukan ruhunku, ranku, da kuma jikinku su zama marar aibi a dawowar Ubangijinmu Yesu Kiristi.
Ibr 13:4Aure yă zama abin girmamawa ga kowa, a kuma kiyaye gadon aure da tsabta, gama Allah zai hukunta masu zina da kuma dukan masu fasikanci.
Kol 3:5Saboda haka, sai ku fid da duk wani abin da yake kawo sha’awa a zukatanku, fasikanci, ƙazanta, sha’awa, muguwar sha’awa, da kuma kwaɗayi wanda shi ma bautar gumaka ne.
Afi 5:17Saboda haka kada ku zama wawaye, sai dai ku fahimci ko mene ne nufin Ubangiji.
Afi 5:3–5Kada a ma ambaci fasikanci, da kowane irin aikin lalata, ko kwaɗayi a tsakaninku, domin bai dace da mutane masu tsarki na Allah ba. Haka ma bai kamata a sami datti, ƙazamar magana, ko zancen banza a cikinku ba, domin ba su dace ba, a maimakon haka sai ku yi ta yin godiya. Ku dai tabbata, ba wani mai fasikanci, ko mai aikin lalata, ko mai kwaɗayin (wanda shi da mai bautar gumaka ɗaya ne), da yake da gādo a mulkin Kiristi da na Allah.
Gal 5:19Ayyukan mutuntaka kuwa a fili suke. Wato, fasikanci, ƙazanta da kuma lalata;

Tushe: OpenBible.info, CC BY 4.0 · Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi