Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Shahararrun ayoyin Littafi Mai Tsarki › Afisawa 4:29

Ayar Littafi Mai Tsarki · SRK

Afisawa 4:29

Kada wata ƙazamar magana ta fita daga bakunanku, sai dai abin da yake da amfani don gina waɗansu bisa ga bukatunsu. Ta haka maganarku za tă zama da amfani ga masu jinta.

Karanta dukan babin: Afisawa 4

A cikin mahallinsa

26“Cikin fushinku kada ku yi zunubi.” Kada ku bar rana ta fāɗi kuna fushi,

27kada kuma ku ba wa Iblis dama.

28Duk wanda yake sata, sai yă daina sata, dole kuma yă yi aiki, yă yi wani abu mai amfani da hannuwansa, don yă sami abin da zai iya raba da masu bukata.

29Kada wata ƙazamar magana ta fita daga bakunanku, sai dai abin da yake da amfani don gina waɗansu bisa ga bukatunsu. Ta haka maganarku za tă zama da amfani ga masu jinta.

30Kada kuma ku ɓata wa Ruhu Mai Tsarki na Allah rai, wanda da shi aka hatimce ku da shi don ranar fansa.

31Ku rabu da kowane irin ɗacin rai, haushi da hasala, faɗa da ɓata suna, ku rabu da kowace irin ƙeta.

32Ku yi alheri, ku kuma ji tausayin juna, kuna gafarta wa juna, kamar yadda a cikin Kiristi, Allah ya gafarta muku.

Afisawa 4

Da Turanci

Berean Standard BibleEphesians 4:29Let no unwholesome talk come out of your mouths, but only what is helpful for building up the one in need and bringing grace to those who listen.

Nassoshi masu alaƙa

Sassan da masu karatu suka fi danganta wa da wannan.

Kol 4:6Bari maganarku kullum ta zama da ladabi da kuma daɗin ji, domin ku san amsar da ta dace ku ba wa kowa.
1Tes 5:11Saboda haka ku ƙarfafa juna ku kuma gina juna, kamar dai yadda kuke yi.
M Had 10:12Kalmomi daga bakin mai hikima alheri ne, amma maganganun wawa za su hallaka shi.
K Mag 15:7Leɓunan masu hikima sukan baza sani; ba haka zukatan wawaye suke ba.
Kol 3:8–9Amma yanzu dole ku raba kanku da dukan ire-iren abubuwan nan. Ku daina fushi, ku daina ƙiyayya da ƙeta. Ku bar ɓatan suna da kuma ƙazamar magana daga leɓunanku. Kada ku yi wa juna ƙarya, da yake kun tuɓe tsohon halinku tare da ayyukansa
Mat 12:34–37Ku macizai, ta yaya ku da kuke mugaye za ku iya magana kirki? Gama daga baki, mutum yakan faɗi abin da yake cikin zuciya. Mutumin kirki yakan fito da abubuwa masu kyau daga ajiyar da aka a yi cikinsa, mugun mutum kuwa yakan fito da mugayen abubuwa daga cikin muguntar da aka yi ajiya a cikinsa. Amma ina gaya muku cewa mutane za su ba da lissafi a ranar shari’a a kan kowace kalmar banza da suka faɗa. Gama ta wurin kalmominka za a kuɓutar da kai, kuma ta wurin kalmominka za a hukunta ka.”
K Mag 25:11–12Kalmar da aka faɗa daidai tana kamar zubin zinariyar da aka yi a mazubin azurfa. Kamar ’yan kunnen zinariya ko kuwa kayan ado na zinariya zalla haka yake da tsawatawar mai hikima ga kunne mai saurarawa.
Zab 37:30–31Bakin mutum mai adalci yakan yi magana da hikima, harshensa kuwa yakan yi maganar abin da yake daidai. Dokar Allahnsa tana a cikin zuciyarsa; ƙafafunsa ba sa santsi.

Tushe: OpenBible.info, CC BY 4.0 · Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi