Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Shahararrun ayoyin Littafi Mai Tsarki › Afisawa 4:26–27

Ayar Littafi Mai Tsarki · SRK

Afisawa 4:26–27

26“Cikin fushinku kada ku yi zunubi.” Kada ku bar rana ta fāɗi kuna fushi,

27kada kuma ku ba wa Iblis dama.

Karanta dukan babin: Afisawa 4

A cikin mahallinsa

23A maimakon haka, bari Ruhu yă sabunta tunaninku da kuma halayenku.

24Ku sanya sabon halin nan da aka halitta bisa ga kamannin Allah, halin nan kuwa, yă bayyana cikin adalci, da zaman tsarki.

25Saboda haka dole kowannenku yă bar yin ƙarya, yă kuma riƙa faɗa wa maƙwabcinsa gaskiya, gama dukanmu gaɓoɓi jiki ɗaya ne.

26“Cikin fushinku kada ku yi zunubi.” Kada ku bar rana ta fāɗi kuna fushi,

27kada kuma ku ba wa Iblis dama.

28Duk wanda yake sata, sai yă daina sata, dole kuma yă yi aiki, yă yi wani abu mai amfani da hannuwansa, don yă sami abin da zai iya raba da masu bukata.

29Kada wata ƙazamar magana ta fita daga bakunanku, sai dai abin da yake da amfani don gina waɗansu bisa ga bukatunsu. Ta haka maganarku za tă zama da amfani ga masu jinta.

30Kada kuma ku ɓata wa Ruhu Mai Tsarki na Allah rai, wanda da shi aka hatimce ku da shi don ranar fansa.

Afisawa 4

Da Turanci

Berean Standard BibleEphesians 4:26–27“Be angry, yet do not sin.” Do not let the sun set upon your anger, and do not give the devil a foothold.

Ambato daga Tsohon Alkawari

Zab 4:4Cikin fushinku kada ku yi zunubi; sa’ad da kuke kan gadajenku, ku bincike zukatanku ku kuma yi shiru. Sela

Nassoshi masu alaƙa

Sassan da masu karatu suka fi danganta wa da wannan.

Yaƙ 1:19’Yan’uwana ƙaunatattu, ku lura da wannan. Ya kamata kowa yă kasance mai saurin saurara, ba mai saurin magana ba, ba kuma mai saurin fushi ba,
Zab 37:8Kada ka yi fushi kada kuma ka yi hasala; kada ka tsorata, wannan yakan kai ga mugunta ne kawai.
Afi 4:31–32Ku rabu da kowane irin ɗacin rai, haushi da hasala, faɗa da ɓata suna, ku rabu da kowace irin ƙeta. Ku yi alheri, ku kuma ji tausayin juna, kuna gafarta wa juna, kamar yadda a cikin Kiristi, Allah ya gafarta muku.
Yaƙ 4:7Saboda haka, ku miƙa kanku ga Allah. Ku yi tsayayya da Iblis, zai kuwa guje ku.
M Had 7:9Kada ranka yă yi saurin tashi, gama fushi yana zama a cinyar wawaye.
K Mag 14:29Mutum mai haƙuri yana da fahimi mai yawa, amma mai saurin fushi yakan nuna wautarsa a fili.
K Mag 19:11Hikimar mutum kan ba shi haƙuri; ɗaukakarsa ce ya ƙyale laifi.

Tushe: OpenBible.info, CC BY 4.0 · Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi