Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Shahararrun ayoyin Littafi Mai Tsarki › Afisawa 5:15–17

Ayar Littafi Mai Tsarki · SRK

Afisawa 5:15–17

15Sai ku yi hankali sosai da yadda kuke rayuwa, kada ku zama kamar marasa hikima, sai dai kamar masu hikima.

16Ku kuma yi matuƙar amfani da kowane zarafi, don kwanakin nan mugaye ne.

17Saboda haka kada ku zama wawaye, sai dai ku fahimci ko mene ne nufin Ubangiji.

Karanta dukan babin: Afisawa 5

A cikin mahallinsa

12Gama abin kunya ne a ma faɗi abubuwan da marasa biyayya suke yi a ɓoye.

13Duk abin da aka kawo a gaban haske ana iya ganinsa, kuma duk abin da aka haskaka yakan zama haske.

14Shi ya sa aka ce, “Ka farka, ya kai mai barci, ka tashi daga matattu, Kiristi kuwa zai haskaka ka.”

15Sai ku yi hankali sosai da yadda kuke rayuwa, kada ku zama kamar marasa hikima, sai dai kamar masu hikima.

16Ku kuma yi matuƙar amfani da kowane zarafi, don kwanakin nan mugaye ne.

17Saboda haka kada ku zama wawaye, sai dai ku fahimci ko mene ne nufin Ubangiji.

18Kada ku bugu da ruwan inabi, wanda yake kai ga lalaci. A maimako haka, ku cika da Ruhu.

19Ku yi zance da juna cikin zabura, da waƙoƙi, da kuma waƙoƙin ruhaniya. Ku rera, ku kuma yi kiɗe-kiɗe a zuciyarku ga Ubangiji.

20Kullum ku dinga yin amfani da sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi, kuna gode wa Allah Uba a kome.

Afisawa 5

Da Turanci

Berean Standard BibleEphesians 5:15–17Pay careful attention, then, to how you walk, not as unwise but as wise, redeeming the time, because the days are evil. Therefore do not be foolish, but understand what the Lord’s will is.

Nassoshi masu alaƙa

Sassan da masu karatu suka fi danganta wa da wannan.

Kol 4:5Ku zama masu hikima a yadda kuke ma’amala da waɗanda suke ba masu bi ba; ku kuma yi amfani da kowane zarafi.
Rom 12:2Kada ku ci gaba da yin abin da duniya take yi, sai dai ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so yake, abu mai kyau, mai daɗi da kuma cikakke.
Yaƙ 3:13Wane ne mai hikima da fahimta a cikinku? Bari yă nuna ta ta wurin rayuwarsa mai kyau, ta wurin ayyukan da aka yi cikin tawali’un da suke fitowa daga hikima.
Amos 5:13Saboda haka mai hankali yakan yi shiru a lokuta kamar haka, gama lokutan mugaye ne.
Yoh 12:35Sai Yesu ya ce musu, “Haske zai kasance da ku na ɗan lokaci. Ku yi tafiya yayinda hasken yana nan tare da ku, kada duhu yă cim muku. Mai tafiya a cikin duhu bai san inda za shi ba.
Fil 1:27Kome ya faru, ku yi zaman da ya cancanci bisharar Kiristi. Ta haka, ko na zo na gan ku, ko ban zo ba, in ji labari cewa kun tsaya da ƙarfi a cikin ruhu ɗaya, kuna fama kamar mutum ɗaya saboda bangaskiyar bishara
1Kor 14:20’Yan’uwa, ku daina tunani kamar yara. Wajen mugunta ku zama jarirai, sai dai wajen tunaninku, ku zama manya.
1Tes 5:18ku yi godiya cikin kowane hali, gama wannan shi ne nufin Allah dominku cikin Kiristi Yesu.

Tushe: OpenBible.info, CC BY 4.0 · Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi